Gwamnatin tarayya na shirin fadada NHIS - Osinbajo

Gwamnatin tarayya na shirin fadada NHIS - Osinbajo

Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasar Najeriya ya ce gwamnatin tarayya na shirin fadada shirin inshoran lafiya na kasa (NHIS) domin kula da lafiyan 'yan Najeriya.

Mataimakin shugaban kasar ya yi wannnan jawabin ne a a wurin taron kaddamar da tsarin inshoran lafiya na jihar Bauchi a ranar Asabar.

"Za mu fadada shirin NHIS a cikin mataki na gaba domin mu tabbatar dukkan 'yan Najeriya sun samu kulawa ta fannin lafiya," inji shi.

Gwamnatin tarayya na shirin fadada NHIS - Osinbajo

Gwamnatin tarayya na shirin fadada NHIS - Osinbajo
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Su daure mu idan mun yi sata - Gwamnan APC mai barin gado

Ya ce akwai bukatan dukkan gwamnatocin jihohi su kafa nasu shirin samar da inshoran lafiya domin tallafawa na gwamnatin tarayya wurin samar da ingantataccen kulawa ga lafiyar 'yan Najeriya.

Osinbajo ya ce jihar Bauchi itace tafi amfana da shirin gwamnatin tarayya na tallafawa 'yan kasa da rage radadin talauci wato NSIP.

"Matasa 14,075 na jihar Bauchi suna amfana da shirin N-Power yayin da daliban makarantun frimare 618,214 ne ake ciyarwa a kullum karkashin shirin ciyar da daliban makaranta," inji mataimakin shugaban kasar.

"A kalla manoma 9,799 sun samu bashi mai saukin biya karkashin shirin micro credit, 'yan kasuwa 29,000 sun samu tallafi karkashin shirin trader moni yayin da mutane 23,000 na amfana da tallafin gwamnati na mutane masu karamin karfi.

"Dukkan wadannan hanyoyi ne da shugaban kasa ke kullawa ta talakawan Najeriya."

Tunda fari, Gwamna Muhammed Abubakar na jihar ya ce shirin inshoran lafiyar ya taimakawa jama'ar jiharsa samun ingantaccen kulawa cikin sauki.

Abubakar ya ce shirin zai taimakawa talakawa da masu hannu da shuni samun saukin kula da lafiyarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel