Tsohon zakaran dan kwallon Afirka, Yaya Toure ya sagale takalmin kwallo

Tsohon zakaran dan kwallon Afirka, Yaya Toure ya sagale takalmin kwallo

Fitaccen dan kwallon kafa daga nahiyar Afirka kuma tsohon zakaran kwallon kafa a nahiyar Afirka, Yaya Toure ya kammala shirye shiryen yin murabus daga murza Tamola a karshen kakan kwallon kafa ta bana, kamar yadda wakilinsa, Dimitri Seluk ya bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Seluk ya bayyana cewa Yaya zai karkatar da hankalinsa ne wajen horas da yan wasa da iya tafiyar dasu, a yanzu, sa’annan ya kara da cewa dan kwallon ya ajiye kwallo ne yana dan shekara 35.

KU KARANTA: Shariff Rabiu Usman Baba: Muhimman batutuwa 10 game da rayuwarsa

Tsohon zakaran dan kwallon Afirka, Yaya Toure ya sagale takalmin kwallo

Yaya Toure
Source: UGC

Yaya ya taka leda a manyan kungiyoyin kwallon kafa da suka hada da Barcelona, Monaco, Manchester City, Olympiakos da kuma uwa uba kungiyar kwallon kafa ta kasar Ivory Coast, inda ya taka rawar gani matuka a dukkanin timatiman.

A kungiyar Barcelona kadai, Yaya Toure ya taimaka musu wajen lashe kofin Laliga guda daya, da kuma kofin zakarun nahiyar Turai watau Champions League, daga nan ya koma Manchester City a shekarar 2010 inda ya lashe kofin Firimiya guda uku, Carling biyu da kofin FA guda daya.

Sai dai Seluk yace sun tattauna batun yin murabus na Yaya Toure sosai, kuma ya dade yana bukatar yin murabus din tun bayan wasan karshe daya buga a kungiyar kwallon kafa ta Manchester City.

“A shekara 35 wasu yan kwallon sun gwammace su cigaba da taka leda, amma ni da Yaya mun dauki shawara na daban, don haka muka yake shawarar duk wanda ya buga ma Barcelona da Manchester City kamata yayi ya shiga horas da yan kwallo.

“Ina fatan zai rawar gani a matsayinsa na mai horas da yan kwallo musamman a Afirka da kuma gasar Firimiya, inda babu wani dan Afirka dake horas da yan wasa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel