Lafiya jari: Amfanin citta biyar a jikin dan Adam

Lafiya jari: Amfanin citta biyar a jikin dan Adam

Citta na daya daga cikin kayan kamshi masu dauke da sinadarai da ke amfanar da jikin bil adama. Bayan ga karin lafiya citta na da dandano mai kamshi da ke karawa abinci, shayi ko abin sha armashi.

Sinadari mafi muhimmanci a cikin cita shi ne Gingerol. Gingerol yana da matukukar amfani kuma shine ke sanya dandanon yaji da ake ji a citta.

Ana iya amfani da danyen citta, ko busashe ko kuma a matse ruwansa domin a sha. Duk da cewa masanna sunyi itifaki a kan amfanin da citta ke da shi, yana da kyau mutum ya tuntubi likitansa kafin ya yi amfani da citta mai yawa musamman mata masu juna biyu da masu shayarwa.

Lafiya jari: Amfanin citta biyar a jikin dan Adam

Lafiya jari: Amfanin citta biyar a jikin dan Adam
Source: UGC

Ga amfanonin citta kamar haka:

1 - Taimakawa wurin sarrafa abinci: Citta na taimakawa wurin sarrafa abincin da muka ci kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen karfafa garkuwan jiki. Citta na tsarkake bakin mutum ta hanyar samar da yawu wanda ke taimakawa wurin sarrafa abinci.

2 - Magance zafin ala'dar mata (Dysmenorrhea): Galibin mata sukan yi fama da ciwon ciki yayin da al'adarsu na wata ya zo kuma daya daga cikin abubuwan da ake amfani da shi wurin saukake zafin ciwon shine citta. Ana iya shan ruwan citta kafin al'ada ko bayan an gama al'adan.

DUBA WANNAN: Su daure mu idan mun yi sata - Gwamnan APC mai barin gado

3 - Yaki da cutar daji da rage tsufa: Citta na dauke da wasu sinadarai masu yaki da cututuka a jiki wanda ake kira 'Antioxidants' wanda suke taimakawa wurin magance kansa musamman ta mahaifa. Kazalika, antioxidant na taimakawa wurin kare fatar jikin dan adam daga lakumewa.

4 - Magance tashin zuciya: Akwai tarihi da binciken masanana masu yawa game da amfani da citta wurin magance tashin zuciya da rashin sha'awan cin abinci. Hakan na faruwa ne saboda citta yana hana tashin zuciya da amai.

5 - Daidaita adadin siga a jinin dan Adam: Binciken masana ya nuna cewa citta yana taimakawa wurin daidaita yawan siga a jinin mutum. Wannan yana da muhimmanci saboda yawan siga da ke jinin dan adama yana da alaka da kara kiba ko rage kiba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel