Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un: Rabiu Usman Baba ya rasu

Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un: Rabiu Usman Baba ya rasu

Da sanyin safiyar Alhamis, 9 ga watan Mayu wanda yayi daidai da 4 ga watan Ramadan muka samu rahoton cewa Allah Ya yi ma fitaccen sha'irin nan, Sheriff Rabiu Usman Baba rasuwa.

Legit.ng ta ruwaito za’a gudanar da Jana’izarsa a yau Alhamis a gidansa dake kofa ta biyu watau Second Gate dake unguwar Janbulo cikin garin Kano.

KU KARANTA: Jama’tu Nasril Islam ta koka ga Buhari game da tabarbarewar tsaro a Najeriya

Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un: Rabiu Usman Baba ya rasu
Rabiu Usman Baba
Asali: Facebook

Kafin rasuwarsa, Rabiu Usman Baba ya shahara wajen rera wakokin yabo ga Manzon Allah da Iyalansa, inda har ya ciri tuta kuma ya zamo shugaban kungiyar mawakan Manzon Allah, watau Shu’ara’ul Islam ta Najeriya gaba daya.

Zuwa yanzu dai jama’a da daman a cigaba da bayyana alhininsu game da mutuwar babban sha’irin, tare da jimamin rashinsa, musamman duba da yadda wakokinsa suka yi tasiri a tsakanin mabiya darikar Tijjaniyyah da Kadiriyya.

Wasu daga cikin fitattun wakokin Rabiu Usman Baba sun hada da Tauhidi Babu tantama, Tsumagiya, sha yabo, majalisi, wakar Sadiya, zumunci, tambaya, sharifai, Fadima, Garkuwa, Batijaniya, Bakadiriya, Fiyayya, Sayyadil Wara da Zuma.

Da fatan Allah Ya jikansa da gafar, da dukkanin Musulman da suka rigamu gidan gaskiya, Amin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel