An tura 'zauna gari banza' gidan yari saboda taba nonon kwaila

An tura 'zauna gari banza' gidan yari saboda taba nonon kwaila

A ranar Laraba ne wata kotun Majistare da ke zamanta a Igbosere a Legas ta yanke wa wani mutum, Ilias Mudashiru hukuncin zaman gidan yari na watanni shida saboda taba nonon wata budurwa tare da kaiwa 'yan uwanta hari.

Alkalin kotun, F.O Sasanya ta yanke wa Mudashiru bayan ya amsa laifinsa na tuhumar hadin baki, cin zarrafi da duka da ta haifar da rauni.

Wannan laifukan sun sabawa sashi na 173, 263 (i) da 411 na dokar masu laifi na jihar Legas na 2015.

An tura 'zauna gari banza' gidan yari saboda taba nonon kwaila
An tura 'zauna gari banza' gidan yari saboda taba nonon kwaila
Asali: Twitter

Ta yanke wa Mudashiru hukunci ne bayan ta gama sauraron hujojin da dan sanda mai shigar da kara, Godspower Ehizoha ya gabatarwa kotu.

DUBA WANNAN: Kotun Shari'a za ta datse hannun mutum 10, a jefe 5 a Bauchi

An gurfanar da Mudashiru ne a ranar 26 ga watan Afrilu.

Tunda farko, Ehizoha ya shaidawa kotu cewa wanda aka gurfanar a gaban kotun ya aikata laifin ne a ranar 21 ga watan Afrilu misalin karfe 8.20 na safe a kasuwar Bombata, layin Oroyinyin a unguwar Adeniji Adele a jihar Legas.

Ya ce Mudashiru ya hada baki da wasu wadanda har yanzu ba su shigo hannu ba domin cin mutuncin Judith Nwachima ta hanyar taba mata nono a yayin da ta ke hanyar ta na zuwa asibiti.

Ehizoba ya ce a lokacin da Mudashiru ya ke cin zarafin Nwachima, 'yan uwanta guda biyu, Stanley Chinedu da Asoiba Chinedu sunyi yunkurin kawo mata dauki amma Mudashiru ya daba musu kwalba a kai, wuya da hannu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164