Dalilin da ya sa za mu gudanar da bincike a kan Saraki - EFCC

Dalilin da ya sa za mu gudanar da bincike a kan Saraki - EFCC

Hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, ta fidda wani sabon rahoto domin zayyana dalilan ta na fara gudanar da bincike akan shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki a yayin da ya rike akalar jagoranci ta gwamnatin jihar Kwara.

Domin tabbatar da tsayuwar dakan ta wajen tsarkake kasar nan daga dukkanin miyagun ababe masu yiwa tattalin arziki zagon kasa, hukumar EFCC ta dukufa wajen gudanar da bincike akan shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki.

A ranar Talatar da gabata, shugaban majalisar dattawa ya yi zargin cewa binciken da hukumar EFCC za ta gudanar a kan tsohuwar gwamnatin sa yayin kasancewar sa gwamnan jihar Kwara na da nasaba da wata kitimurmura.

Abubakar Bukola Saraki
Abubakar Bukola Saraki
Asali: Depositphotos

Saraki wanda ya kasance daya daga cikin manyan jiga-jigai na kasa a jam'iyyar adawa ta PDP, ya rike akalar jagoranci ta gwamnatin jihar Kwara cikin tsawon wa'adi biyu a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011.

Cikin sakon ta na mayar da martani a ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2019, baya ga babu wanda ya fi karfin shari'a, tsari da tanadin doka, hukumar EFCC ta ce binciken da ta dukufa wajen gudanar wa a kan tsohuwar gwamnatin Saraki na da madogara ta cikar muradin al'umma.

Duk da cewa Saraki na cikakken 'yanci na bayyana ra'ayin sa akan hukumar, EFCC ta ce bincike a kan sa zai ci gaba da gudana domin tabbatar da magarcin jagoranci wajen karkatar da dukiyar al'umma ta hanya mafi dace.

KARANTA KUMA: Jonathan ya yi watsi da jam'iyyar PDP a zaben 2019

Yayin tumke damara na tabbatar da wannan kudiri, hukumar EFCC a ranar Litinin da ta gabata ta nemi samun masaniya daga gwamnatin jihar Kwara a kan duk wasu alherai na dukiya da Saraki ya samu yayin riko da akalar jagoranci ta jihar.

Ku tuna cewa a makon da ya gabata ne shugaban majalisar dattawan Najeriya ya samu nadin mukami na jakadan hukumar kare hakkin bil Adama ta kasa-da-kasa, International Human Rights Commission.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel