Soyayya: Kishi ya tunzura wani saurayi ya kashe abokin ‘takararsa’

Soyayya: Kishi ya tunzura wani saurayi ya kashe abokin ‘takararsa’

Wata kotun majistri dake zamanta a garin Ado-Ekiti ta daure wani matashi mai suna Abdullahi Lawal mai shekaru 35 sakamakon tuhumarsa da ake yi da kashe abokin takararsa a wajen budurwar da yake kauna.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Lawal ya kashe Olaoluwa Fayomi mai shekaru 50 a rayuwa ne saboda zarginsa da yake yi na neman budurwarsa, a dalilin haka rikici ya kaure a tsakaninsu har ta kai ga ta caka masa wuka a kirji.

KU KARANTA: Mutane 5 sun mutu a sanadiyyar harin yan bindiga a jahar Taraba

Dansanda mai shigar da kara, Oriyomi Akinwale ya bayyana ma kotu cewa Lawal ya aikata wannan aika aika ne a ranar 24 ga watan Afrilun shekarar 2019, ya kara shaida ma kotu cewa budurwar ta fada ma Lawal cewa soyayyarsu ta kare, kuma ta fara soyayya da Fayomi.

A cewar Dansanda Akinwale, bayan budurwar ta bayyana ma Lawal sabon saurayinta ne sai Lawal ya fara neman shi da rikici, inda har ta kaiga wata rana sun buga, anan ne Lawal ya samu damaya caka masa wuka a kirji, nan take Fayomi ya fadi matacce.

Dansandan ya bayyana ma kotu cewa laifin da ake tuhumar Lawal da aikatawa ya saba ma sashi na 319 (1) na kundin dokokin jahar Ekiti na shekarar 2012, don haka ya nemi kotun ta daure Lawal har sai sun samu shawara daga ofishin babban mai shigar da kara na jahar Ekiti.

Daga karshe bayan sauraron dukkanin bangarorin, Alkalin Kotu, mai sharia Modupe Afeniforo ta bada umarnin a garkame mata Lawal, sa’annan ta dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Yuni don cigaba da shari’ar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel