A yau hutun Buhari na kwanaki 10 a kasar Ingila ya kare

A yau hutun Buhari na kwanaki 10 a kasar Ingila ya kare

Hutun kwanaki 10 da shugaba Buhari ke yi a kasar Ingila zai kare a yau, Lahadi, 5 ga watan Mayu, kamar yadda fadar shugaban kasa ta sanar.

Tun kafin tafiyar shugaba Buhari, kakakinsa, Femi Adesina, ya sanar da cewar shugaban kasar zai bar gida Najeriya a ranar 25 ga watan Afrilu, sannan ana saka ran zai dawo ranar 5 ga watan Mayu.

A cikin jawabin, Adesina ya ce; "shugaba Buhari zai wuce zuwa Ingila a wata ziyara ta musamman da zai kai kasar bayan ya kammala ziyarar aiki a jihar Borno. Zai dawo gida Najeriya a ranar 5 ga watan Mayu."

Sai dai, a yayin da ziyarar shugaba Buhari ta kare a ranar Lahadi, babu tabbacin ko zai dawo gida Najeriya kamar yadda kakakinsa ya sanar a baya ko kuma zai kara wa'adin zaman sa a kasar.

A yau hutun Buhari na kwanaki 10 a kasar Ingila ya kare
Buhari da iyalinsa a cikin jrigi
Source: Twitter

Kwanaki 10 da Buhari ya shafe a Ingila, su ne suka kawo jimillar kwanakin da ya yi a kasar zuwa 227 a tsawon shekaru hudu da ya yi yana mulkin Najeriya.

Shugaba Buhari ya ziyarci kasar Ingila a tsakanin ranakun 5 zuwa ga 10 ga watan Fabarairu a shekarar 2016, ya ziyarci kasar ne domin halartar wani taro a kan yaki da cin hanci.

Bayan halartar wannan taro, Buhari ya kara ziyartar kasar Ingila a cikin shekarar ta 2016 domin neman maganin ciwon kunne.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai hari gidan tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa

Buhari ya kara koma wa kasar Ingila daga ranar 19 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Maris na shekarar 2017, inda ya yi zaman jinya.

Watanni biyu bayan dawowar sa, Buhari ya kara koma wa kasar Ingila inda ya shafe tsawon kanaki 104, daga ranar 8 ga watan Mayu zuwa ranar 19 ga watan Agusta.

Buhari ya kara koma wa kasar Ingila domin yin hutunsa na karshen shekara daga ranar 9 zuwa 21 ga watan Mayu.

A watan Mayu na sahekarar 2018, shugaba Buhari ya yi wata gajeriyar tsayawa a kasar Ingila. Kazalika, ya ziyarci kasar Ingila daga ranar 8 zuwa 11 ga watan Mayu, sannan ya kara koma wa kasar daga ranar 3 zuwa 18 ga watan Agusta, duk a cikin shekarar 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel