Matsaloli 10 da shan sanyi ke haddasawa

Matsaloli 10 da shan sanyi ke haddasawa

Duba ga yanayin zafi da ake ciki a yanzu da dama daga cikin jama’a kan bukaci shan abu mai sanyi ko ruwa mai sanyi ko kuma dai zama a waje mai sanyi duk don ganin sun samu saukin zafi a tattare da su.

Sai dai yawaita aikata hakan na da matukar illa ga lafiyar jikin dan Adam, kamar yadda likitoci suka yi bayani.

Masana harkar lafiya sun bayyana cewa yawaita shan ruwa mai sanyi ko kuma zama a wuri mai sanyi kan sa a kamu da cutar hakarkari, Sanyin kashi, toshewar murya, mura da dai sauran su.

Domin guje wa kamuwa da wadannan matsalolin kamata ya yi a rage yawan shan ruwan sanyi da zama a wuri mai sanyi.

Matsaloli 10 da shan sanyi ke haddasawa
Matsaloli 10 da shan sanyi ke haddasawa
Asali: UGC

Ga wasu illolin da shan ruwan sanyi da yawan zama a wuri mai sanyi ke kawowa.

1. Shan abu mai sanyi na janyo kamuwa da mura.

2. Shan sanyi na sa mutum ya kamu da sanyin kashi.

3. Sanyi kan toshe wa mutum murya da haddasa cutrar makogoro.

4. Akan haifi yaran dake dauke da cutar hakarkari wato ‘Pneumonia’ da turanci.

5. Yawan shan ruwan sanyi na rage karfin mazakutan namiji sannan ya hana mace haihuwa.

6. Yana kawo ciwon koda.

7. Yana hadasa ciwon kai mai tsanani.

KU KARANTA KUMA: Kungiyoyin Musulunci sun jinjina wa gwamnatin tarayya kan sakin Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar

8. Shan ruwan sanyi na saurin busar da ruwan jikin mutum illa ya kara sa mutun jin kishin ruwa.

9. Yana lalata tsarin hanjin cikin mutum inda haka ke hana abinci narkewa a ciki.

10. Yana rage karfin jiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng