Kungiyoyin Musulunci sun jinjina wa gwamnatin tarayya kan sakin Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar

Kungiyoyin Musulunci sun jinjina wa gwamnatin tarayya kan sakin Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar

- Kungiyoyin addinin Musulunci sun yaba ma gwamnatin tarayya akan kokarinta wajen ceto Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar wanda hukumomin kasar Saudiyya suka tsare

- An dai kama Zainab da Ibrahim Abubakar a kasar Saudiyya a ranar 25 ga watan Disamba, 2018, bayan an samu miyagun kwayoyi a jakunkunansu

- Sai dai an gano cewa ma'aikatan filin jirgi ne suka yi masu bita da kulli

Kungiyoyin addinin Musulunci a ranar Juma’a 3 ga watan Mayu sun yaba ma gwamnatin tarayya akan kokarinta wajen ceto Miss Zainab Aliyu da Mista Ibrahim Abubakar wanda hukumomin kasar Saudiyya suka tsare.

An kama Zainab da Ibrahim Abubakar a kasar Saudiyya a ranar 25 ga watan Disamba, 2018, bayan an samu miyagun kwayoyi a jakunkunansu.

Ma’aikatar da ke kula daharkokin waje ta tabbatar da sakin Abubakar a ranar Laraba da ya gabata.

Kungiyoyin Musulunci sun jinjina wa gwamnatin tarayya kan sakin Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar

Kungiyoyin Musulunci sun jinjina wa gwamnatin tarayya kan sakin Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar
Source: Facebook

An mika Abubakar ga mukkadin karamin jakada Najeriya a Jeddah, kasar Saudiyya, Garba Satomi Grema.

Yayinda ita kuma Zainab an sake ta ne a ranar Talatar da ta gabata.

Kungiyoyin Musuluncin sun bayyana cewa yan Najeriya sun yi farin ciki da sanya bakin da gwamnatin tarayya tayi a lamarin.

KU KARANTA KUMA: Kasar Saudiyya ta yi kira ga a fara neman jaririn watan Ramadan daga gobe Asabar

kungiyar NASFAT ta jinjina wa gwamnati da jakadan Najeriya a kasar Saudiyya kan kokarinsu wajen ceto yan kasar.

Mista Banji Busari, sakataren labarai na NASFAT, ya bayyana cewa ya kamata a gudanar da bincike a tsanaki domin gano wadanda suka sanya kwayoyin a jakunkunansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel