Za a samu karuwar marasa aikin yi a Najeriya - FG

Za a samu karuwar marasa aikin yi a Najeriya - FG

Yawan marasa aiki a Najeriya zai yi tashin gwauron zabi daga kaso 23.1 zuwa 33.5 zuwa shekarar 2020, a cewar gwamnatin gwamnatin tarayya.

Ministan kwadago da samar da aiyuka, Sanata Chris Ngige, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da yake gabatar da jawabi a wurin bude wani taro a kan yadda za a shawo matsalar rashin aikin yi a Najeriya.

Ya bayyana hauhawar alkaluman marasa aiki a matsayin abin damuwa ga kasa bakidaya.

Ministan ya bayyana cewar gwamnatin tarayya ta damu matuka bayan hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewar yawan marasa aiki a Najeriya ya kai kaso 16.6% a shekarar 2019.

Za a samu karuwar marasa aikin yi a Najeriya - FG

Chris Ngige
Source: Depositphotos

Ngige ya ce: "abin damuwa ne matuka, kamar yadda bankin duniya ya fada a shekarar 2018, akwai alaka mai karfi tsakanin rashin aikin yi da hauhawar aiyukan ta'addanci da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, tu'ammali da miyagun kwayoyi da sauran su.

DUBA WANNAN: EFCC ta gurfanar da wani mutum da ya kashe fiye da miliyan 200 da aka tura asusun sa bisa kuskure

"Amma duk da wadannan matsaloli da rashin aiki ke haifar wa, alkaluma sun yi hasashen cewar yawan marasa aiki a Najeriya zai yi tashin gwauron zabi daga kaso 23.1% zuwa kaso 33.5 a cikin shekarar 2020. Akwai bukatar a dauki matakan gagga wa domin shawo kan wannan babbar matsala."

Ministan ya kara da cewa sanin illar dake tattare da rashin aikin yi ne ya saka gwamnatin su dage wa wajen kirkirar guraben aiyuka da hanyoyin rage yawan masu zaman kashe wando.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel