Jirgin makarantar koyon tuki ya yi saukar bazata a Ilorin

Jirgin makarantar koyon tuki ya yi saukar bazata a Ilorin

Matukan jirgin sama biyu na makarantar koyon tukin jirgi a jihar Kwara a ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, sun tsallake rijiya da baya bayan wani jirgin horo mallakar makarantar ya fado a filin jirgin saman Ilorin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jirgin na Diamond mai lamba 5N-BNH dauke da matukan jirgi biyu ya fado da misalin karfe 11:15am, a ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, ba tare da kowa ya mutu ba.

Lamarin ya haifar da tashin hankali a fili jirgin saman da garin Ilorin. An tattaro cewa jami’in IAC da wasu ma’aikatan filin jirgin na wajen da lamarin ya afku wanda ya shafi ayyukan tashin jirage na tsawn sa’o’i uku.

Jirgin makarantar koyon tuki ya yi saukar bazata a Ilorin
Jirgin makarantar koyon tuki ya yi saukar bazata a Ilorin
Source: UGC

Gwamnan jihar Abdulfatah Ahmed wanda zai koma gida daga tafiyar da yayi zuwa Abuja ya samu jinkiri sakamakon lamarin. A lokacin wannan rahoton, an tattaro cewa an sanar da sashin bincike lamarin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun karyata batun sace dalibai a makarantar mata na Zamfara

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Hukumar tashoshin jiragen sama na Najeriya (FAAN) ta janye jami’anta da ke samar da tsaro daga hatsarruka da kashe gobara daga tashoshin jiragen sama na Gombe da Kebbi akan bashin fiya da naira miliyan 732 da ake bin su.

Babban Manajan harkokin hukumar FAAN, Misis HenrietteYakubu, ta tabbatar da lamarin ga kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu a Legas.

Yakubu tace janye ayyukan FAAN daga tashoshin jiragen saman, wanda yayi sanadiyar tsayar da ayyukan tashin jiragen sama ya fara ne daga ranar 1ga watan Mayu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel