Buhari ya jinjinama masu yiwa kasa hidima saboda jajircewarsu

Buhari ya jinjinama masu yiwa kasa hidima saboda jajircewarsu

- Buhari ya yabawa masu yiwa kasa hidima saboda jajircewa kan aiki

- Masu bautar kasa na kawo cigaba daban-daban a sassan kasar nan, inji Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinama masu yiwa kasa hidima bisa ga aiki tukuru da sukeyi domin kawo cigaba a sassa da dama na kasar nan.

Buhari yayi wannan jawabin ne yayinda ake wani taro na musamman domin karrama wasu daga cikin masu yiwa kasa hidima sakamakon kawo wani sauyi a wuraren da suka kasance yayin bautar kasa. Wannan taro ya gudana a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Buhari ya jinjinama masu yiwa kasa hidima saboda jajircewarsu

Buhari ya jinjinama masu yiwa kasa hidima saboda jajircewarsu
Source: UGC

KU KARANTA:Gwamnatin tarayya ta kashe N3.5trn wurin ayyukan gine-ginen raya kasa a shekara 3, inji Osinbajo

Daga cikin wadanda aka karrama da lambar yabo a wurin taron sun hada da: tsofaffin masu yiwa kasa hidima su 15 wadanda suka samu nakasa a lokacin bautan kasar.

Buhari wanda mataimakinshi Yemi Osinbajo ya wakilta ya nemi wadannan masu lalura da kada su karaya su cigaba da ganin kawunansu a matsayin shugabanni da kuma jakadun NYSC.

Ya kara yaba masu bisa ga nuna jajircewa a lokacin da suke bautar kasa inda yake cewa tabbas kun cancanci yabo kyakkyawa.

Shugaban ya kara da cewa duk da dai shugabanci nauyine da kuma dawainiya ta jama’a, sai dai nasan zaku iya duba zuwa ga nasarar da kuka samu a lokacin da kuke yiwa kasa hidima. A don haka nasara na tare daku har zuwa gaba a wuraren da zaku tsinci kawunanku.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel