Bakin ciki ya saka wata tsaleliyar daliba ta kashe kanta

Bakin ciki ya saka wata tsaleliyar daliba ta kashe kanta

- Tsananin bacin rai da bakin ciki rayuwa ya tilasta wata daliba shan guba ta kashe kanta

- Dalibar wacce ke aji daya a jami'ar Port Harcourt, dake jihar Rivers ta kashe kanta ne ta hanyar shan kwalba biyu na guba

Wata daliba da ke aji daya a fannin kirkire-kirkire a jami'ar Port Harcourt, da ke jihar Rivers, ta kashe kanta, bayan ta yi ta fama da bakin ciki na lokaci mai tsawo.

Dalibar da aka bayyana sunanta da Hikmat Gbadamosi an samu gawarta a kwance a cikin dakinta, a cewar kawarta, marigayiyar ta na fama da matsalar rashin lafiya tun lokacin da aka haifeta, kuma matsalar rashin lafiyar ce ta saka ta a cikin halin matsanancin bakin ciki na rayuwa.

Bakin ciki ya saka wata tsaleliyar daliba ta kashe kanta

Bakin ciki ya saka wata tsaleliyar daliba ta kashe kanta
Source: Facebook

Alamu sun nuna cewa dalibar ta sha kwalba biyu na guba a ranar Asabar 27 ga watan Afrilun nan, kuma ba a ga gawarta ba sai jiya Litinin 29 ga watan Afrilu. An samu gawarta dinne sanadiyyar babbar aminiyarta ta tattara 'yan ajinsu akan su je dakinta su tambayeta menene dalilin da yasa ba ta je makaranta ba jiya.

KU KARANTA: Jihohi 23 da za su biya ma'aikatansu albashin N30,000 a Najeriya

Shigarsu gidan kenan sai suka ga kofar dakin ta a rufe, sai suka leka ta taga sai suka ga gawarta a kwance. A lokacin suka kira taimakon mutane aka karya kofar dakin nata.

Makwabtan ta sunce ranar Asabar ne ganin da suka yi mata na karshe. Sunce akwai yiwuwar dalibar ta mutu ranar Asabar dinne da daddare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel