CBN ta ba wasu sababbin bankuna 5 lasisin fara aiki

CBN ta ba wasu sababbin bankuna 5 lasisin fara aiki

A cikin makon nan ne mu ka samu labari daga Jaridar Business Day ta kasar nan cewa babban bankin Najeriya na CBN ya bada lasisi ga wasu bankuna da ake shirin kafawa domin su fara aiki.

Kamar yadda labari ya zo mana a Ranar 29 ga Watan Afrilun nan, bankuna 5 ne masu neman tasowa aka ba lasisin soma aiki a Najeriya. CBN ta dauki wannan mataki ne domin ganin ana shigo da kudi ana juyawa a Najeriya.

Wannan sababbin lasisi da CBN ya raba zai kuma taimkawa mutanen da ba su mallaki asusun banki ba, su samu damar bude akawun domin su rika ajiye kudin su a cikin banki. Hakan zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

KU KARANTA: Za a sake shiga cikin matsin tattali a Najeriya - Gwamna Yari

Akwai fiye da mutane miliyan 50 da ba su aiki da banki a halin yanzu a Najeriya, kamar yadda hasashe ya nuna. Wasu daga cikin bankunan nan za su fara aiki a watan gobe, yayin da wasun za su soma aiki a tsakiyar shekarar nan.

Globus wanda yana cikin bankin da za a bude a kasar, zai shigo gari ne a Ranar Alhamis dinnan, 2 ga Watan Mayun 2019. Elias Igbinakenzua shi ne babban Darektan wannan banki da za a kafa Hedikwatar sa a cikin Garin Legas.

KU KARANTA: Manyan Jami’an Gwamnati na yunkurin sace Biliyoyi kafin Buhari ya zarce

Haka zalika akwai wani banki da nutanen kasar Indiya su ka kawo Najeriya mai suna Titan Bank. Wani tsohon Darektan bankin nan na Heritage, shi ne zai soma rike wannan banki na kamfanin Chi wanda su kayi fice a fadin Duniya.

Ana tunani cewa wannan sabon bankin na Titan zai rika hulda ne da mutanen Indiya da kuma kwarorin kasar Lebanon da ke ayyuka a Najeriya. Har yanzu dai babu wanda ya san sunayen sauran manyan bankuna 3 da su ka samu lasisi.

‘Yan jarida sun yi kokarin tuntubar bankin CBN amma ba a dace ba. Isaac Okarafor, wanda yake magana a madadin bankin bai amsa kiran da aka rika yi masa a waya domin jin ta bakinsa ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel