Jihohi 23 da za su biya ma'aikatansu albashin N30,000 a Najeriya
Ana ta samun karin jihohi a Najeriya wadanda suke nuna cewa suma sun gama shiryawa tsaf domin fara biyan sabon albashin N30,000, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu makonnin da suka gabata
Akwai yiwuwar jihohi ashirin da uku na iya biyan sabon albashi da gwamnatin tarayya ta sanya hannu na naira dubu 30.
Gwamnonin jihohin sunyi magana akan biyan sabon albashin, bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da sabon albashin dokar kasa.
Da yawa daga cikin jihohin sun ce, dole ne a sanya wasu ka'idoji tsakanin ma'aikata da gwamnatin tarayya domin su samu su biya sabon albashin.
Wasu sunce su kawai suna jira gwamnatin tarayya ta gama tsara yadda za a biya albashin, sai su fara biya.
Kungiyar kwadago ta kasa wacce ta yi alkawarin ba za ta taba amincewa da kin biyan ma'aikatan sabon albashin ba, ta ce za ta takura gwamnatin tarayya domin ganin ta gabatar da tsare-tsaren biyan albashin ga jihohi.
A cewar babban sakataren kungiyar kwadagon takasa Dr. Peter Ozo-Eson, ya ce abu na farko da gwamnoni za su fara mayar da hankali a kai bayan an rantsar da su a ranar 29 ga watan Mayu, shine biyan sabon albashi da shugaban kasa ya mayar doka.
KU KARANTA: Kasashe biyar da suka fi ko ina jin dadin rayuwa, da kasashe biyar da suka fi ko ina kuncin rayuwa
Ya ce, duk da haka ba a sa ran dukkanin jihohin kasar nan za su biya sabon albashin ga ma'aikatan su.
Ga jerin jihohin da suka nuna cewa sun shirya tsaf domin fara biyan sabon albashin ma'aikatan a kasa:
- Kano
- Zamfara
- Osun
- Kwara
- Kogi
- Niger
- Delta
- Rivers
- Edo
- Cross River
- Benue
- Ondo
- Ekiti
- Imo
- Ebonyi
- Enugu
- Anambra
- Oyo
- Ogun
- Katsina
- Sokoto
- Plateau
- Jigawa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng