Ku tabbatar Kiristoci sun zama shugabannin majalisa – Malamai ga yan majalisa

Ku tabbatar Kiristoci sun zama shugabannin majalisa – Malamai ga yan majalisa

Kungiyar Malaman addinin Kirista na Najeriya Christian (CAC-NIG) ta bukaci kiristoci, wadanda aka zaba a majalisar dokokin kasar da su tabbatar da cewa basu bar ma Musulmai shugabancin majalisar dattawa da majalisar wakilai ba.

Kungiyar ta bayyana ra’ayinta bisa lamarin barin Musulmai su shugabanci dukkanin rukunin gwamnati guda uku, ta lura cewa wannan na iya haddasa halaka ga damokardiyyar kasa da tsarin banbanci.

Shugaban kungiyar CAC-NIG na kasa, Archbishop Yiman Orkwar, ya bayyana damuwarsa a wani jawabi wanda kakakinsa, Fasto Ortindi Torough Baka ya gabatar, sannan aka gabatar ga jaridar The Guardian a Makurdi jiya (Lahadi).

Ku tabbatar Kiristoci sun zama shugabannin majalisa – Malamai ga yan majalisa

Ku tabbatar Kiristoci sun zama shugabannin majalisa – Malamai ga yan majalisa
Source: UGC

Ya zargi majalisar harkokin Islama na Najeriya (NSCIA) da goya ma shugaban kasa Muhammadu Buhari baya wajen nuna banbanci a nade-nadensa, inda ya bayyana ikirarin mataimakin sakataren kungiyar, Farfesa Salisu Shehu, na cewa kiristoci sun mamayi majalissun a baya a matsayin munafurci.

KU KARANTA KUMA: Ba talauci bane ya sa ni shiga filin tono ma’adinai ba, neman halal nake – Isa Yuguda

CAC-NIG ta cigaba da gargadi ga NSCIA da ta kula wajen jawabai masu tunzurawa wadanda ke iya saka kasar cikin tashin hankali na addinai, ya kara da cewa kungiyan baza ta amince kungiyoyin musulmai su cigaba nuna batanci ga kungiyar CAN da shugabancinta ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel