Alheri gadon barci: Attajiri ya fara rabon kayan Sallah ga gajiyayyu da talakawa a Sakkwato

Alheri gadon barci: Attajiri ya fara rabon kayan Sallah ga gajiyayyu da talakawa a Sakkwato

Wani shahararren attajiri dan asalin jahar Sakkwato, Alhaji Yahaya Sirridawa kuma jigo a jam’iyyar APC ya rabar da kyautan kayan Sallah da kudi ga talakawa da gajiyayyu, mata da kananan yara a jahar Sakkwato.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sirridawa yayi ma talakawa wannan kabakin alheri ne a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu a gidansa dake cikin garin Sakkwato, inda yace yayi hakan ne kamar yadda ya saba tallafawa tare da taimaka ma gajiyayyu.

Alheri gadon barci: Attajiri ya fara rabon kayan Sallah ga gajiyayyu da talakawa a Sakkwato
Sirridawa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Zaratan Sojoji sun kashe yan bindiga 6, sun kama dakatai 2 masu aikin leken asiri

A cewarsa, wannan taimako yazo a daidai sakamakon karatowar azumin watan Ramadan, kuma sanannen abu ne cewa ana so Musulmi ya yawaita ciyarwa da bayar da taimako a watan Ramadana.

Alheri gadon barci: Attajiri ya fara rabon kayan Sallah ga gajiyayyu da talakawa a Sakkwato
Sirridawa
Asali: UGC

Sai dai Sirridawa yayi kira ga wadanda suka ci gajiyar tallafin dasu yi amfani dasu yadda ya kamata, sa’annan yayi kira ga sauran Attajirai ire irensa dasu daure wajen taimaka ma talakawa don rage musu radadin halin rayuwa.

Daga cikin kayayyakin da attajirin ya rabar akwai shaddodi, atamfofi, da kuma kudi naira dubu biyar biyar, inda aka hangi mabarata, almajirai, da sauran jama’an gari suna rige rigen karbar naso rabon.

Alheri gadon barci: Attajiri ya fara rabon kayan Sallah ga gajiyayyu da talakawa a Sakkwato
Sirridawa
Asali: UGC

A wani labarin kuma yau Litinin, 22 ga watan Afrilu shine yayi daidai da 16 ga watan Sha'aban, wanda hakan ke nufin lissafin kwanakin zuwan watan Azumin Ramadan bai wuce sati biyu ba, ma'ana kwanaki 14.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: