Wasu iyaye sun kashe dansu saboda suna zargin maye ne

Wasu iyaye sun kashe dansu saboda suna zargin maye ne

- An kama wasu mata da miji da laifin kashe dansu mai shekaru 12 a duniya ta hanyar bashi guba,

- Sun bayyanawa hukumar 'yan sanda cewa suna zargin cewa yaron maye ne shine yasa suka kashe shi, saboda duk wata wahala ta rayuwa da suke ciki ta na da nasaba da yaron nan

Jiya ne rundunar 'yan sandan jihar Akwa Ibom ta bayyana wasu 'yan ta'adda guda 16 da ta kama, ciki hadda wani mutum mai suna Essien Okon, wanda ake zargin ya kashe danshi mai suna Joseph, wanda ke da shekaru 12 a duniya.

Ana zargin Essien da matar shi mai suna Peace, da hada wani magani mai guba, suka tilasta yaron akan ya sha.

Hukumar ta ce ta samu labarin cewa mata da mijin sun dauki yaron suka kai shi cikin daji suka binne.

Wasu iyaye sun kashe dansu saboda suna zargin maye ne

Wasu iyaye sun kashe dansu saboda suna zargin maye ne
Source: UGC

Baban yaron wanda bai musanta zargin da ake yi masa ba ya ce, yaron maye ne, kuma shine ya kashe tsohuwar matarshi, wato mahaifiyar shi.

Mun samu labarin cewa Essien ya auri Peace ne bayan mutuwar mahaifiyar Joseph din.

Ya kara da cewa duk wata rashin sa'ar rayuwa da ya ke fuskanta ta na da nasaba da tarayyarshi da yaron.

Kwamishina 'yan sandan jihar, Zaki Ahmed, ya bayyanawa manema labarai cewa za su mika wadanda ake zargin ga kotu don yanke musu hukunci da sun kammala bincike akan su.

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin rataye wasu mutane guda 7

"A ranar 29 ga watan Maris shekarar 2019, jami'an hukumar 'yan sandan jihar suka kama Essien Okon da matar shi Peace Okon, akan layin Edoho Emma, da ke karamar hukumar Oron, da laifin hada baki wurin kashe Joseph, wanda suke zargi da cewa maye ne."

Kwamishinan ya kara da cewa a ranar 4 ga watan Afrilu nan ne, da misalin karfe 1 na safe, jami'an 'yan sandan jihar suka gano wata maboyar masu garkuwa da mutane, a karamar hukumar Etinan, jami'an kuma sun samu nasarar kama gawurtaccen shugaban masu garkuwa da mutane wanda ya addabi mutanen yankin, mai suna Edidiong Bill.

Ya ce bayan sun gabatar da kwakkwaran bincike akan shi ya bayyana cewa shine shugaban duk 'yan ta'addar da suka addabi mutane a yankin karamar hukumar Etinan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel