Mohammed Salah zai tashi daga Liverpool, zai fadi kulob din da zai koma

Mohammed Salah zai tashi daga Liverpool, zai fadi kulob din da zai koma

Wani rahoto daga kafar yada labarai ta AS na nuni da cewar Mohammed Salah, dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ke kasar Ingila, zai bar taka leda a kungiyar Liverpool a karshen zangon kakar wasanni ta bana.

Dan wasan ya cimma matsaya a kan barin Liverpool bayan muhimmiyyar gana wa da kociyan kungiyar, Jurgen Klopp.

Rahotanni sun bayyana cewar Mohammed Salah ne da kan sa ya nemi mahukuntan kungiyar Liverpool da su bashi damar barin Anfiled (filin wasan kungiyar Liverpool) a karshen kakar wasanni.

Har yaznu tauraruwar Salah na haska wa a kungiyar Liverpool a kakar wasanni ta bana.

Mohammed Salah zai tashi daga Liverpool, zai fadi kulob din da zai koma

Mohammed Salah
Source: Getty Images

An dade ana alakanta Salah da canja kulob zuwa wasu manyan kungiyoyi, musamma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ke kasar Spain.

Rahoton na AS ya bayyana cewar Salah ne ya nemi mahukunta a Liverpool da su bashi damar ya tashi bayan wata muhimmiyar tattauna wa da Klopp.

DUBA WANNAN: Gasar zakarun turai: Messi ya yi gaba, Christiano ya koma gida

Sai dai, har yanzu ba a san wacce kungiya Salah ke son koma wa ba. Ana sa ran zai bayyana kungiyar da zai koma a cikin wasikar neman tashi daga Liverpool da zai bawa shugabannin kungiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel