Innalillahi wa inna ilahi raji’un: Anyi jana’izar mutane 16 da yan bindiga suka kashe a Sokoto
Tsugune bata kare ba, yayin da wasu gungun yan bindiga sun afka wasu kauyukan jahar Sakkwato inda suka far ma jama’a mazauna kauyukan, suka kashe mutane goma sha shida, kamar yadda wani ma’abocin shafin Facebook, Ahmad Aliyu ya bayyana.
Majiyar Legit.ng ya ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Talata 16 ga watan Afrilu, inda yan bindigan suka far ma kauyukan Garuwan Surbudu, Tsalluwa da kuma Sabon garin Tsalluwa dake cikin karamar hukumar Isa.
KU KARANTA: Malaman BUK da yan siyasa ne suka kulla magudin da aka yi a zaben Kano – Jega
Haka zalika akwai mutane hudu da suka jikkata a sakamakon harin, wanda a yanzu haka suna samun kulawa a Asibiti, hakanan sun kona rumbunan hatsi guda ashirin (20) da kuma yin awon gaba da shanu arba’in da takwas (48).
Daga hotunan da majiyar namu ya wallafa a shafin nasa na kafar sadarwar zamani ta Facebook ana iya ganin yadda jama’a suka gudanar da jana’iza akan guda daga cikin gawarwakin da yan bindigan suka kashe.
A wani labarin kuma Dakarun rundunar Sojan na musamman sun tarwatsa wasu gungun yan bindiga da suka kaddamar da hare hare a kauyukan Rafi da Dola dake cikin lardin Mada na karamar hukumar Gusau ta jahar Zamfara a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu.
Kaakakin rundunar, Komodo Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace sun samu bayanai dake nuna yan bindigan sun fara tattaruwa a kauyukan Rafi da Dola da nufin kai musu hari, hakan tasa suka garzaya don fafatawa dasu.
Daramola ya cigaba da fadin ba tare da bata lokaci ba suka tura da wasu rukunin dakarun Sojoji na musamman, wanda suka tarwatsa shirin yan bindiga, har ma suka kashe guda biyu daga cikinsu, yayin da sauran suka ranta ana kare dauke da munanan raunuka.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng