Ana shan bakar wuya a mulkin Buhari - Jarumar fim

Ana shan bakar wuya a mulkin Buhari - Jarumar fim

- Omotola, fitacciyar jarumar shirya fina-finan harshen Turanci a kudancin Najeriya, Nollywood, ta 'yan Najeriya na shan bakar wuya a mulkin Buhari

- Jarumar ta nuna bacin ranta a kan kashe-kashen rayuka da 'yan ta'adda ke yi a sassan Najeriya

- Ta yi kira ga gwamnati da ta dauki matakan gagga wa domin magance matsaloli da kalubalen da Najeriya ke fuskanta

Wata fitacciyar jarumar wasan fina-finan kwaikwayo na kudancin Najeriya, Nollywood, mai suna Omotola Jalade, ta soki salon mulkin Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari, inda ta bayyana cewar ‘yan Nijeriya na shan bakar wahala a mulkinsa, sannan ta koka da asarar rayukan da ake samu a wasu sassan kasar nan.

Omotola ta bayyana hakan ne a shafinta na sada zumunta, wato Tuwita, in da ta koka a kan kashe-kashen rayukan jama’ar da basu ji ba, balle su gani ba da ‘yan taadda ke yi.

Ana shan bakar wuya a mulkin Buhari - Jarumar fim
Omotola Jelade
Asali: Twitter

Kazalika ta bayyana kisan farar hula da jami’an tsaro ke yi a matsayin abun takaici, sannan ta kara da cewa matukar gwamnatin Buhari ba ta yi maganin wadannan matsaloli ba, za su iya haifar da wata matsalar mai girman gaske.

DUBA WANNAN: Kin biyan haraji: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin kama Okocha

Omotola ta bukaci gwamnatin Buhari da ta yi wani abu cikin gagga wa a kan halin da kasar nan ke ciki, matukar da gaske gwamnati na son ci gaban kasa da jama’ar cikinta, ta ce kin daukan matakan gagga wa domin magance matsalolin da Najeriya ke ciki, ba zai haifar wa da kasa da mai ido ba

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel