Yan Najeriya 23 na cikin jerin mutanen da za a yanke wa hukuncin kisa a Saudiyya

Yan Najeriya 23 na cikin jerin mutanen da za a yanke wa hukuncin kisa a Saudiyya

Kasar Saudiyya na kare tsarin dokarta bayan jayayyan da ya biyo bayan hukuncin kisa da aka zartar akan wata yar Najeriya, Kudirat Adeshola Afolabi, akan laifin safarar miyagun kwayoyi.

Akalla yan Najeriya 23 ne ke sawun wadanda za a yanke ma hukuncin kisa a masarautar.

Jakadan masarautar Saudiyya, Amb. Adnan Mahmod Bostaji, a jiya Lahadi, yace an zartar da hukuncin ne bayan an samar da hujjoji.

Ya bayyana tsarin dokar a matsayin tsarin gaskiya, ya kuma kara da cewa tsarin yana aiki ne akan gaskiya da adalci.

Ya kara da cewa kimanin yan Najeriya miliyan 1.5 ne ke zaune a kasar Saudiyya ba tare da an muzguna musu ba.

Yan Najeriya 23 na cikin jerin mutanen da za a yanke wa hukuncin kisa a Saudiyya
Yan Najeriya 23 na cikin jerin mutanen da za a yanke wa hukuncin kisa a Saudiyya
Asali: UGC

Bostaji ya roki hukumomi a tashoshin jirgin saman Najeriya da su aiwatar da tsare-tsare da zai hana yin fasa kwarin kwayoyi.

Kasar ta gano wani takarda dauke da jerin sunaye yan Najeriya 23 wadanda za a yi ma hukuncin kisa a Saudiyya.

Wadanda hukuncin kisa ya cika dasu sun hada da: Adeniyi Adebayo Zikri; Tunde Ibrahim; Jimoh Idhola Lawal; Lolo Babatunde; Sulaiman Tunde; Idris Adewuumi Adepoju; Abdul Raimi Awela Ajibola; Yusuf Makeen Ajiboye; Adam Idris Abubakar; Saka Zakaria; da Biola Lawal.

KU KARANTA KUMA: Lamarin tsaro ya tabarbare – Dattawan Arewa

Sauran sun hada da: Isa Abubakar Adam; Ibrahim Chiroma; Hafis Amosu; Aliu Muhammad; Ms. Funmilayo Omoyemi Bishi; Ms. Mistura Yekini; Amina Ajoke Alobi; Kuburat Ibrahim; Alaja Olufunke Alalaoe Abdulqadir; Fawsat Balagun Alabi; Aisha Muhammad Amira; da Adebayo Zakariya.

A cewar takardan, an kama yan Najeriyan da laifuffukan da suka saba ma doka. Kuma a tsarin kasar hukuncin kisa ne ga duk wanda ya keta dokar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel