Naka naka ne: Yadda Buhari ya tarbi yayarsa a fadar shugaban kasa (Hoto)

Naka naka ne: Yadda Buhari ya tarbi yayarsa a fadar shugaban kasa (Hoto)

Masu iya magana na cewa “Dan uwa rabin jiki”, hakan ta tabbata a yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin babbar yayarsa, Hajiya Rakiya a fadar shugaban kasa dake Aso Rock Villa, Abuja.

Legit.ng ta ruwaito Hajiya Rakiya Adamu, wanda itace yaya guda daya tilo da ta rage ma shugaban kasa Buhari ta kai masa wannan ziyara ne a ranar Juma’a, 12 ga watan Afrilu, inda aka hangeta zaune tare da Buharin akan kujera daya.

KU KARANTA: Shugabancin majalisa ta 9: An bayyana Sanatan da gwamnonin APC 24 ke muradi

Naka naka ne: Yadda Buhari ya tarbi yayarsa a fadar shugaban kasa (Hoto)
Buhari da Rakiya
Asali: Facebook

Shi dai shugaba Muhammadu Buhari shine da namiji daya tilo a wajen mahafiyarsa, kuma shine dan auta, yayin da yake da yayyu mata da dama, sai dai dukkaninsu Allah Yayi musu rasuwa, sai Hajiya Rakiya da ta rage masa, hakan yasa suka shaku da juna sosai da sosai.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ma sai da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai mata ziyara a gidanta dake garin Daura ta jahar Katsina, a yayin daya kai ziyarar aiki jahar Katsina. Haka zalika gwamnan jahar Bauchi, M.A Abubakar ma ya kai mata ziyara a yayin wata ziyara daya kai garin Daura.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatarwa Iyayen yaran da aka sace a Makarantar sakandaren nan da ke Garin Chibok cewa bai manta da ‘Ya‘yan su da aka yi gaba da su tun a shekarar 2014 ba.

Buhari ya bayyana haka ne ta bakin kaakakinsa Malam Garba Shehu inda yace bai manta da ragowar wadannan Yara da ke tsare a hannun ‘Yan ta’addan kungiyar Boko Haram ba, kuma yana iya bakin kokarinsa don ganin ya cetosu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel