Yau Sheikh Ja'afar ya ke cika shekaru 12 da rasuwa

Yau Sheikh Ja'afar ya ke cika shekaru 12 da rasuwa

A yau ne fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Arewacin Najeriya, Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ya cika shekaru goma sha biyu da rasuwa.

Wadansu 'yan ta'adda ne suka harbeshi a lokacin da yake jagorantar sallarn asubah a masallaci a jihar Kano, 'yan ta'addar sun harbi malamin a ranar 13 ga watan Afirilun shekarar 2007 wato lokacin ana saura kwana daya ayi zaben gwamnan jihar Kano.

Yau Sheikh Ja'afar ya ke cika shekaru 12 da rasuwa

Yau Sheikh Ja'afar ya ke cika shekaru 12 da rasuwa
Source: Facebook

Marigayin yana daya daga cikin mayan malaman addinin musulunci a bangaren izala wanda ya ke da dumbin mabiya a fadin Najeriya da ma wasu kasashe da suke makwabtaka da Najeriyan.

Duk da cewa har yanzu al'umma su na cigaba da bayyana mutuwar fitaccen malamin a matsayin babban rashi ga al'ummar Najeriya dama duniyar musulunci baki daya, har ya zuwa yanzu dai hukumomin tsaron Najeriya basu binciko mutumin da ya harbi malamin ba.

KU KARANTA: Atiku na cikin tsaka mai wuya

Majiyarmu LEGIT.NG ta binciko wasu muhimman abubuwa guda bakwai dangane da rayuwar fitaccen malamin.

1. An haifi Sheikh Ja'afar ranar 12 ga watan Fabrairun shekarar 1961 a garin Daura cikin jihar Katsina.

2. Ya dawo jihar Kano don koyon karatun Al-Qur'ani, lokacin da ya ke da shekaru hudu a duniya.

3. Sheikh Ja'afar ya fara koyon karatun addini a wurin mijin yayarsa.

4. Sheikh Ja'afar ya haddace Al-Qur'ani mai girma a shekarar 1978

5. Sheikh Ja'afar ya fara karatun boko a shekarar 1990.

6. Fitaccen malamin ya yi karatun addinin Musulunci a kasar Saudiyya da kasar Sudan, inda ya samu digirin sa na biyu.

7. A kowane watan azumi Sheikh Ja'afar ya na komawa garin Maiduguri dake jihar Borno don gabatar da tafsirin karatun Al-Qur'ani mai girma.

Mutuwar Sheikh Ja'afar ta girgiza al'ummar musulman Najeriya, musamman idan aka yi la'akari da irin kisan gillar da aka yi masa. Sai dai kuma hakan bai hana malamin cigaba da suna a duniyar Musulunci ba, saboda da yawan mutane basu san da shi ba sai bayan rasuwar shi.

A karshe majiyarmu LEGIT.NG ta na yi wa malamin addu'ar Allah ya karbi shahadar shi, ya sa ya huta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel