Karbar mulki daga hannun Buhari: FG ta zakulo shedan abinda Atiku ke kulawa da Amurka

Karbar mulki daga hannun Buhari: FG ta zakulo shedan abinda Atiku ke kulawa da Amurka

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ya biya kamfanin Fein & DelValle PLLC da ke Amurka kudi Dallan Amurka 30,000 kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Dan takarar na jam'iyyar PDP ya biya kamfanin kudin ne domin wasu ayyuka da za suyi masa a yunkurin da ya ke yi na amshe mulki daga hannun Shugaba Muhammadu Buhari.

Cibiyar nazarin siyasa 'Centre for Responsive Politics' (CRP) ta ruwaito yadda Atiku ya dauki hayar wani tsohon ma'aikacin hukumar shari'a na Amurka mai suna Bruce Fein da kamfaninsa Fein & DelValle PLLC a watan Maris.

A cikin yarjejeniyar da suka kulla, Fein & DelValle PLLC ta ce za ta bude dakin bincike a Amurka a ofishinta da ke Amurka inda za su rika aiki tare da wani lauya dan Najeriya kuma na hannun daman Atiku mai suna Lloyd Ukwu.

DUBA WANNAN: Zargin Madigo: Yadda Hadiza Gabon ta titsiye Amina Amal, ta rika zagba mata mari

Kamfanin kuma ta ce za ta tabbata cewa gwamnatin Amurka ta goyi bayan yunkurin da Atiku keyi na kwace mulki daga hannun Buhari a zaben da ta ce an tafka mugudi da tashin hankali da jam'iyyar APC da tayi yayin zaben.

Karbar mulki daga hannun Buhari: FG ta zakulo shedan abinda Atiku ke kulawa da Amurka

Karbar mulki daga hannun Buhari: FG ta zakulo shedan abinda Atiku ke kulawa da Amurka
Source: Twitter

Sai dai kwana guda bayan wallafa rahoton, Atiku ya musanta cewa ya biya wani kamfanin Amurka kudi a yunkurinsa na karbar mulki daga Buhari.

A sanarwar da ya fitar da bakin kakakinsa Paul Ibe, tsohon shugaban kasar ya ce rahotannin da ake yadawa na cewa ya biya wata kamfani $30,000 'karya ne.'

Ya yi ikirarin cewa APC ne ke son kulla masa sharri domin su shafa masa kashin kaza.

Sai dai takardan da The Cable ta wallafa ya nuna cewa Atiku ya biya kamfanin kudin kwanaki biyu bayan sanya hannu kan yarjejeniyar kwanaki 90 (Daga ranar 1 ga watan Afrilu zuwa 1 ga watan Yulin 2019). Ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar a ranar 24 ga watan Maris sannan ya biya kudin a ranar 26 ga watan Maris.

Karbar mulki daga hannun Buhari: FG ta zakulo shedan abinda Atiku ke kulawa da Amurka

Karbar mulki daga hannun Buhari: FG ta zakulo shedan abinda Atiku ke kulawa da Amurka
Source: Twitter

Za ayi amfani da kudin ne domin sayan kayaykin aiki na kwanaki 90 din. Kazalika, yarjejeniyar ta ce Atiku zai sake biyan dukkan kudaden tafiye-tafiye na kasa da kasa.

Kawo yanzu, Kakakin Atiku bai amsa tambayoyin da majiyar Legit.ng tayi masa ba game da sabon takardar da ta fito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel