Shugabancin majalisa: Zamu yiwa masu butulci ritaya - APC

Shugabancin majalisa: Zamu yiwa masu butulci ritaya - APC

- APC ta bayyana cewa za ta kora duk mutumin da ya saba ma zabinta na shugabancin majalisar dokokin kasa na tara

- Jam’iyyar ta sabi Sanata Ahmerd Lawan a matsayin wanda take so ya zama Shugaban majalisar dattawa

- Amma Sanata Ali Ndume ya sha alwashin cewa zai yi takarar kujerar duk da zabin jam’iyyar

Mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, yankin Arewa ta Tsakiya, Ahmed Wambai, ya bayyana cewa duk dan jam’iyyar ya yi adawa da hukuncin jam’iyyar dangane da zabin shugabancin majalisar dokokin kasar zai fuskanci hukunci akan rashin biyayya.

Mista Wambai, a wani hira da yayi da manema labarai a Lafia, ya bukaci mambobin jam’iyyar a majalisar dokoki da su yi biyayya ga hukuncin jam’iyyar a dukkan lokuta.

Haka zalika, ya daura laifi ga kafofin sadarwa bisa tallata lamarin shugabancin majalisan dokokin kasar.

Ya kuma musanta batun cewa jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, na bada umurni da kuma tursasa hukunci akan jam’iyyar musamman akan lamari da ya shafi shugabancin majalisar dokokin kasar.

A cewarshi, anyi lauje cikin nadi a jawabin da Mista Tinubu ya gabatar cewa duk wanda bai amince da Femi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisa ba ya fice daga jam’iyyar.

Shugabancin majalisa: Zamu yiwa masu butulci ritaya - APC

Shugabancin majalisa: Zamu yiwa masu butulci ritaya - APC
Source: Facebook

Mista Wambai ya bayyana cewa jam’iyyar ta yanke shawarar cewa Ahmed Lawan ne zai riki matsayin shugaban majalisar dattijai bayan tattaunawa da aka gudanar da masu ruwa da tsaki.

KU KARANTA KUMA: Shehu Sani ya bayyana dalilin da zai sa yayi nasara a kotun zabe

Ya ce shawaran tafiya da Lawan ya kasance akan irin biyayyarsa ga jam’iyyar kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shawarar.

Ya kara da cewa jam’iyyar bata yanke shawara ba a halin yanzu akan mukamin kakakin majalisar wakilai kamar yanda wassu ke cewa Mista Gbajabiamila ne zabin jam’iyyar domin basu da masaniya kan ayyukan cikin gida da APC ke gudanarwa.

Ya kara da cewa jam’iyyar zata hukunta duk wanda ya ki amincewa da shawaran.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel