A hankali a hankali zamu janye tallafin man fetir – Ministan kudi

A hankali a hankali zamu janye tallafin man fetir – Ministan kudi

Gwamnatin Najeriya ta hau kan turbar janye tallafin da take sanyawa akan farashin man fetir, da nufin janyeshi a hankali hankali ba tare da tayar da kura ba, kamar yadda ministan kudi, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Shamsuna ta bayyana haka ne yayin da take jawabi a yayin taron babban bankin duniya da bankin lamuni ta duniya suka shirya, inda shugabar bankin lamuni, Christine Lagarde ta shawarci Najeriya da ta janye tallafin man fetir, ta yadda zata iya amfani da kudaden da take kashewa a tallafin zuwa wasu fannoni kamarsu kiwon lafiya, ilimi da sauransu.

KU KARANTA: Kana da labarin Matar da tafi kowacce mace arziki a duk fadin Najeriya?

Sai dai Hajiya Shamsuna ta mayar ma Lagarde martani, inda tace babu yadda za’ayi a janye tallafin mai a Najeriya a zuwa daya, “Shawara ce mai kyau, amma dole ne muyishi ta yadda zai dawwama, kuma zai haifar da da mai ido.

“Dolene sai mun ilimantar da yan Najeriya tare da wayar musu da kai game da abubuwan da zamu gudanar musu don maye gurbin amfanin tallafin mai a wajensu, don haka aiki ne babba, kuma sai dai ya kasance sannu a hankali.” Inji ta.

Haka zalika ministar ta bukaci bankin duniya ta duba yiwuwar sauya sharuddan data gindaya ma kasashe wajen samun rancen kudaden da zata kashesu a samar da manyan ayyuka, sharuddan da tace suna kawo tsaiko ga yadda ake gudanar da manyan ayyuka.

A wani labarin kuma hadimin shugaban kasa akan harkar samar da ayyuka ga matasa, Afolabi Imoukhuede ya tabbatar ma matasan dake cin gajiyar tsarin daukan aiki na gwamnatin tarayya na N-Power cewa zasu sau albashinsu na watan Maris cikin satin nan.

Afolabi ya bada wannan tabbaci ne a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, yayin da yake musanta zargin da wasu ke yi na danganta nukusanin biyan albashin ga dabarar dakatar da biyan N-Power gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel