Batan N38bn: Yan majalisar wakilai sun sanya manyan jami’an PenCom a kwana na tsawon sama da sa’o’i 3

Batan N38bn: Yan majalisar wakilai sun sanya manyan jami’an PenCom a kwana na tsawon sama da sa’o’i 3

Kwamitin majalisar wakilai da ke binciken hukumar kudin fansho na kasa, a jiya Laraba, ta sanya tawagar hukumar a kwana kan zargin batan kudi naira biliyan 38 wanda babban bankin kasa (CBN) ta sakar mata.

Tsawon sama da sa’o’i uku tawagar majalisar karkashin jagorancin Ehiozuwa Agbonnayinma ya dauka yana gasa tawagar hukumar.

Wani wakilin mukaddashin darakta janar na hukumar Penom, Mista Olohinmi Lana ya dauki aikin amsa mafi akasarin tambayoyin da kwamitin binciken ke yi.

Shugaban kwamitin ya bayyana cewa kwamitin ta bukaci takardar jawabin asusun bankin hukumar, rubuce-rubucen taron tattaunawar hukumar da dai sauran takardun.

Dan majalisan ya bayyana ewa dalilin biniken shine domin a gyara barnar da ke hukumar da kuma kawo ci gaban kasar cewa ba wai akan mayyar-farauta bane.

Ya bayyana cewa jami’ai da dama da suka yi ritaya sun mutu a yayin kokartin ganin sun samu hakkinsu shekaru da dama bayan ritaya.

Batan N38bn: Yan majalisar wakilai sun sanya manyan jami’an PenCom a kwana na tsawon sama da sa’o’i 3
Batan N38bn: Yan majalisar wakilai sun sanya manyan jami’an PenCom a kwana na tsawon sama da sa’o’i 3
Asali: Depositphotos

Agbonayinma ya bayyana cewa kowani jami’i zai tsufa zai kuma yi ritaya wata rana, idan har ba a gyara lamarin ba a yanzu, batun samun kudin sallama zai kara kamari ga tsoffi.

Ya fbayyana cewa sauran hukumomin wadanda suka hada da CBN, Ofishin Babban Akanta na kasa, shugaban ma’aikatu,Sakataren Gwamnatin Tarayya da masu gudanarwa a hukumar Fansho, PFA sun gabatar da takardun da zasu amfani kwamitin.

A cewar shi, wassu takardun sun saba ma bayanai da PenCom ta gabatar bisa zargin bacewar naira biliyan 33 yayin sauraran karan.

Shugaban kwamitin ya bayyana cewa binciken ya kasance layi guda da yunkurin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ganin an kau da cin hanci da rashawa a kasar.

Ekanem Asuquo (PDP-Akwa-Ibom) ya zargi PenCom akan jinkiri da aka samu wajen binciken saboda rashin bada hadin kai.

Ya bayyana cewa halayen hukumar PenCom ga kwamitin ba daidai bane saboda hakan ba zai kyautata ma kasan ba kamar yanda kowa zai tsufa wata rana.

KU KARANTA KUMA: Tawagar lauyoyin APC sun shirya tsaf don kare nasarar Ganduje

A bayaninshi bisa zargin bacewar kudade, shugaban sashin PenCom, Mrista Loyinmi Lana ya bayyana cewa akwai tsare tsare da ya kamata kudade su bi kafin su kai mataki na karshe inda masu ritaya zasu samu kudin sallama.

Ya bayyana cewa a wassu lamarin, sauran hukumomin kamar ofishin Babban Akanta na Kasa sun kasance da hannu cikin tsarin wanda Gwamnatin Tarayya zata dauki nauyi.

Akan gaza gabatar da takardun da kwamitin ta bukata, Lana ya fada cewa akwai shubuha a wasikun kwamitin.

Ya bayyana cewa kwamitin bata bukaci takardan bayanan asusun banki na musamman ba amman ta bukaci shaida akan ayyukan hukumar a lokacin da aka bukata.

Duk da haka, ya bayyana cewa hukuman zata gabatar da takardun shaida masu muhimmanci a ranar 11 ga watan Afrilu.

Majalisar wakilai a watar Disamba 2018 ta yanke shawaran binciken ayyukan hukumar PenCom daga watan Afrilu 2017 zuwa yanzu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel