Hansti leka gidan kowa: Kungiyar Izala ta shilla kasar Amurka don aikin Da’awah

Hansti leka gidan kowa: Kungiyar Izala ta shilla kasar Amurka don aikin Da’awah

Kungiyar jama’atil izalatil bidi’a wa iqamatissunnah ta sanar da isar manyan Malamanta da shuwagabanninta kasar Amurka domin gudanar da aikin Da’awah kamar yadda suka saba yi lokaci zuwa lokaci.

Legit.ng ta ruwaito kungiyar ta bayyana haka ne a shafinta kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda ta daura hotunan shugaban kungiyar Izala, Sheikh Bala Lau, tare da sakataren kungiyar Sheikh Kabiru Gombe yayin da suka isa kasar Amurka.

Hansti leka gidan kowa: Kungiyar Izala ta shilla kasar Amurka don dikin Da’awah

Bala Lau
Source: Facebook

KU KARANTA: Yan bindiga sun halaka mutane 18 tare da barnata dimbin dukiya a Katsina

Sai dai kungiyar ta bayyana cewa shuwagabannin Izalan sun tafi kasar Amurka ne domin gudanar da wa’azuzzuka bayan samun gayyata daga kungiyoyin Musulmai dake kasar Amurka.

Hansti leka gidan kowa: Kungiyar Izala ta shilla kasar Amurka don dikin Da’awah

Kabiru Gombe
Source: Facebook

Anan ana iya ganin hotunan Sheikh Bala Lau tare da Kabiru Gombe a filin sauka da tashin jirage na tunawa da tsohon shugaban kasar Amurka, JF Kennedy dake Birnin New York, a lokacin da suka shigar kasar kenan.

Idan za’a tuna kimanin shekara daya data gabata kenan da shuwagabannin Izala suka kai kwatankwacin wannan ziyara ta Da’awah zuwa kasashen nahiyar Turai, inda suka gabatar da wa’azuzzuka ga Musulman wadannan kasashe.

Daga cikin kasashen da Malaman suka ziyara akwai birnin Hamburg, na kasar Jamus, birnin Landan na kasar Ingila, birnin Andalusia da Basalona a kasar Sifen, da kuma kasar Greece.

Sai dai wannan ziyara ta Malaman Izala kasar Amurka ta tayar da kura a shafinta na Facebook, inda wasu ke ganin ziyarar Da’awan tayi daidai, yayin da wasu kuma ke ganin Malaman sun zake dayawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel