An kama wani mutum dauke da hannuwan Yan Adam a jaka

An kama wani mutum dauke da hannuwan Yan Adam a jaka

- Jihar Ekiti ta na daya daga cikin jihohin da suke fama da matsalar tsaro a kasar nan, musamman 'yan kungiyar asiri, masu garkuwa da mutane da 'yan bingida da suka addabi jihar

- Hukumar 'yan sandan jihar tana iya bakin kokarin ta wurin ganin ta kawo karshen ta'addancin a yankin amma abin ya ci tura

Hukumar 'yan sandan jihar Ekiti sun yunkura wurin kamo masu sayar da sassan jikin mutane, tun lokacin da suka kama wani saurayi dan shekara 23 dauke da hannuwan mutane a cikin jaka Ijero cikin jihar Ekiti.

A rahoton da mai magana da yawun hukumar 'yan sandan ya bayar, Caleb Ikechukwu ya ce, saurayin mai suna Nifemi, an kama shi da hannuwan mutane a cikin jaka. A lokacin da jami'an 'yan sandan suke gabatar da binciken kan hanya ranar Asabar 6 ga watan Afrilu a Ijero Ekiti.

An kama wani mutum dauke da hannuwan mutane a jaka

An kama wani mutum dauke da hannuwan mutane a jaka
Source: UGC

An kama wanda ake zargin a lokacin da ya ke kan hanyar shi ta zuwa Okemesi.

A yanzu dai an kara matakan tsaro a yankin, tun satin da ya gabata, bayan 'yan bindiga da suka addabi mutanen yankin.

Jihar Ekiti dai ita ma tana daya daga cikin jihohin da suke fama da matsalar tsaro, musamman ta fannin 'yan kungiyar asiri da kuma masu garkuwa da mutane. Duk da cewa jami'an tsaro suna iya bakin kokarin su wurin kawo karshen abun a yankin, amma har yanzu abin yaci tura.

KU KARANTA: Muhimman abubuwan da ba ku sani ba dangane da CP Wakili

Mista Nifemi ya boye hannuwan mutanen a cikin jakar ta shi a lokacin da yake kan hanyar shi ta zuwa inda zai hadu da wadanda zai sayarwa da hannayen. Ya kuma bayyanawa jami'an 'yan sandan cewar ya samu hannayen ne a wani wuri mai suna Asa Farmstead, kusa da Okemesi.

Mista Ikechukwu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Litinin a Ado Ekiti, ya bayyana cewa wanda ake tuhumar yana daya daga cikin irin mutanen da suke yanke sassan jikin mutum su sayar, saboda wata manufa ta su ta daban.

Ya kuma kara da cewa yanzu haka ana gabatar da bincike akan wanda ake tuhumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel