Wani mutumi ya hau dokin zuciya ya tafka ma abokinsa danyen aiki

Wani mutumi ya hau dokin zuciya ya tafka ma abokinsa danyen aiki

Wata kotun majistri dake zamanta a garin Ebute Meta ta yanke ma wani mutumi mai suna Rasaki Banjo mai shekaru 51 hukuncin zaman gidan kaso bayan an gurfanar dashi a gabanta kan tuhumarsa da ake yi da zargin kashe abokinsa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkalin kotun, A.O Salawu ce ta bada wannan umarni a ranar Juma’ar data gabata, inda ta nemi a daure mata Rasaki a gidan kurkukun Ikoyi, har zuwa lokacin da babban jami’I mai shigar da kara na jahar Legas ya bada shawarar matakin daya dace da shariar.

KU KARANTA: Dalilin da yasa gwamnonin Najeriya basa zama a jahohinsu – Shehu Sani

Yarsanda mai shigar da kara, Maria Dauda ta bayyana cewa Rasaki ya aikata wannan laifi ne a yayin rikici daya barke a tsakaninsu a ranar 24 ga watan Maris a gida mai lamba 3 daka titin Babayemi cikin unguwar Oworonshoki na jahar Legas.

Yarsandan ta bayyana cewa Rasaki mai shekaru 51 ya fasa kwalba ne ya caka ma abokinsa mai shekaru 41, Enitan Apangbon a wuya, wanda hakan yayi sanadin kwararar jininsa, har sai da yace ga garinku nan.

A cewar Yarsandan, laifin ya saba ma sashi na 223 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Legas na shekarar 2015, wanda tace hukuncinsa na nan a sashi na 223 na kundin hukunta laifukan, wanda ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya aikata irin wannan laifi.

Sai dai bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Alkali Salawu ta dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Mayu.

A wani labarin kuma an kai hankali nesa a karamar hukumar Oshimili ta kudu jahar Delta, inda aka dambace tsakanin shugaban karamar hukumar, Mista Uche Osadebe da kansilolinsa akan zarginsa da suke yi da wawuran kudin yakin neman zabe da gwamnan jahar, Ifeanyi Okowa ya bayar.

Guda daga cikin daraktocin karamar hukumar ya bayyana cewa rikici ya fara tasowa ne yayin da ake saura kwanaki uku da zabe, lokacin da kansilolin suka nemi Ciyaman ya basu rabonsu daga kudin zaben da gwamnan ya baiwa karamar hukumar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel