Ra'ayoyin jama'a kan kalaman Dangote

Ra'ayoyin jama'a kan kalaman Dangote

Tun bayan wannan hira, jama'a da dama na ta bayyana ra'ayoyinsu kan wannan gajeran labarin da mai kudin ya bayar.

Al’umman Najeriya da daman a ci gaba da tofa albarkacin bakunansu akan wasu kalamai da mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya yi.

A hirar da yayi da gidauniyar Mo Ibrahim, Dangote ya bayyana cewa ya taba tattaki zuwa banki inda ya karbo dala miliyan 10 don tabbatar da cewa da gaske yana da kudi.

Ra'ayoyin jama'a kan kalaman Dangote
Ra'ayoyin jama'a kan kalaman Dangote
Asali: UGC

Sai dai ya bayyana cewa ya mayar da kudin banki a washe garin ranar domin ci gaba da killacesu.

KU KARANTA KUMA: Yarimomi 15 na zawarcin kujerar Etsu Patigi

Ga wasu daga cikin ra’ayoyin yan Najeriya kan lamarin:

Wani ma suna Misbah Hamza Ahmad yace: “ Ni randa na gansu da ido na ai sumewa zanyi in aka yayyafan ruwa na farfado kuma na barke da gudawa in zawon na wanka sai na kwanta akan kudin nayi ta sharara kuka .....Naga lailatul Qadari.”

Fatima Tijjani Yerima: “Hmm hakane...! To amma dakagama kallonsu zanso ace karabarwa Talakawan garinkuu dakasamu Lada kwarai dagaske me tarin yawaa...! Kodayake yanzuma waje bekuremaka ba, da zakadagye kayi hakan dakatemaki mutane dayawa maybe ma sanadin hakan Ubangiji yabaka gidan Aljanna... Domin wasu dayawansu sunanan cikin mawuyacin hali suna tsananin bukatar hakan.

Lameer Madugu: “dole kamore tunda Allah ne yabaka....nakane bana alumma ba.”

Mohammad Saleh Yero: “Inama Ace Daka Kirani Nima Inba Idona Abinci.”

Khaleel Shafi'u Habib: “Hakan dakayi kayi daidai Aliko uban nera”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel