Yanzu Yanzu: Sule Lamido da dansa sun nemi kotu ta saki fasfot dinsu

Yanzu Yanzu: Sule Lamido da dansa sun nemi kotu ta saki fasfot dinsu

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma tsohon dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sule Lamido, dansa da wasu mutane uku sun yi wani rubutu da ke neman kotu ta saki fasfot dinsu na tafiya waje.

Legit.ng ta tatatro cewa TransparencIT Nigeria ta bayyana hakan a shafinta na Twitter a ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu.

A cewar TransparencIT Nigeria, kotun ta karbi shaidu dake nuna asusun wanda ake zargi maqare da kudin, a shariar zargin wawure N1.3b.

Legit.ng ta rahoto a baya cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Juma’a, 5 ga watan Afrilu, tace ta samu Karin takardu daga hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) a matsayin hujja akan Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, da sauran mutanen da ake tuhuma.

KU KARANTA KUMA: An matsa wa Goje kan ya amince da Lawan a matsayin Shugaban majalisar dattawa

Lamido na fuskantar tuhuma tare da wasu yaransa biyu masu suna Aminu Sule Lamido da Mustapha Sule Lamido.

Sauran da ke fuskantar tuhuma tare dashi sun hada da Aminu Wada Abubakar, da wasu kamfanoni biyu masu suna Bamaina Holdings Limited and Speeds International Limited.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel