Wutar rikicin kabilanci tsakanin Tibabe da Jukunawa na cigaba da ruruwa

Wutar rikicin kabilanci tsakanin Tibabe da Jukunawa na cigaba da ruruwa

Fadan kabilanci tsakanin kabilun Tibabe da Jukunawa na cigaba da sanadiyyar salwantar rayuka da dama da barnata dukiyoyi a jahar Taraba, inda a wannan karo rikicin ya barke a karamar hukumar Wukari ta jahar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito rikicin na kwana kwanan nan ya barke ne a kauyukan dake iyaka da jahar Taraba da na Benuwe, inda kabilun biyu suke da rinjaye duka, kamar yadda shugaban karamar hukumar Wukari, Daniel Adi ya bayyana.

KU KARANTA: Kotun kolin Najeriya ta shiga halin rudani bisa rahoton ajiye aiki na Alkalin Alkalai

Wutar rikicin kabilanci tsakanin Tibabe da Jukunawa na cigaba da ruruwa
Taraba
Asali: UGC

A jawabinsa a ranar Lahadi, Mista Adi yace akalla kauyuka guda 9 aka tasa daga aiki, yayin da mutane goma suka gamu da ajalinsu, sai kuma wasu adadi masu yawa da suka samu munanan rauni a sanadiyyar rikicin.

“A yanzu haka da nake magana, an kona gidajen mutane da dama, har ma da makarantar sakandarin jeka ka dawo dake garin Kente, an konata kurmus a ranar Lahadi, nayi kokarin kaiwa ga shugaban karamar hukumar Ukum na jahar Benuwe domin ya ja hankalin jama’ansa dasu ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya.” Inji shi.

Sai dai dan takarar gwamnan jahar Benuwe a inuwar jam’iyyar APC, Cif David Kente ya yi tir da wannan rikici, inda ya bayyana cewa a shekarar 1991 kabilun biyu suka fara baiwa hammata iska a garin Kente, amma yayi alkawarin taimaka ma duk wadanda rikicin ya shafa.

Shima kaakakin rundunar Yansandan jahar Taraba, ASP David Misal ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace a yanzu haka rundunar ta aika da jami’an kwantar da tarzoma yankin don kwantar da hankulan jama’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel