Zamafara: Jami'an sa kai na CJTF sun yi fito na fito da 'yan ta'adda, an kashe mutane 50

Zamafara: Jami'an sa kai na CJTF sun yi fito na fito da 'yan ta'adda, an kashe mutane 50

- Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Alhaji Sanusi Rikiji, ya ce akalla mutane 50 da suka hada da jami'an sa kai na CJTF aka kashe a jihar

- Ya alakanta mutuwar da wani yunkuri da jami'an CJTF suka yi na yin fito na fito da 'yan ta'adda a karamar hukumar Kauran Namoda da ke a jihar

- Alhaji Rikiji ya bukaci masu rike da sarautun gargajiya da su gargadi mambobin CJTF akan ayyukan da suka wajaba akansu da wadanda ba huruminsu ba

Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Alhaji Sanusi Rikiji, a ranar Juma'a ya ce akalla mutane 50 da suka hada da jami'an sa kai na CJTF aka kashe a jihar Zamfara a ranar Talata.

Rikiji, wanda ya bayyana hakan a yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai fadar sarkin Kauran Namoda, ya alakanta mutuwar da wani yunkuri da jami'an CJTaf suka yi na yin fito na fito da 'yan ta'adda da suka addabi al'ummar karamar hukumar Kauran Namoda da ke a jihar.

Kakakin majalisar, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa kai ziyarar, ya koka kan yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a jihar.

"Mun samu labarin cewa mambobin jami'an sa kai na JTF sun hada kan wasu jama'a daga garin Sakajiki a karamar hukumar Kauran Namoda kuma sun yi fito na fito da 'yan ta'addan a dajin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 50 da suka hada da jami'an CJTF," a cewar sa.

KARANTA WANNAN: Sanata Kabiru Gaya ya tsaya takarar mataimakin shugaban majalisar dattijai

Zamafara: Jami'an sa kai na CJTF sun yi fito na fito da 'yan ta'adda, an kashe mutane 50
Zamafara: Jami'an sa kai na CJTF sun yi fito na fito da 'yan ta'adda, an kashe mutane 50
Asali: UGC

Rikiji, wanda shi ne shugaban kwamitin yin nazari kan asara da kuma bayar da tallafi na gwamnatin jihar, ya bayyana wannan mataki da CTJF suka dauka a matsayin kunar bakin wake, yana mai cewa "yin fito na fito da yan ta'adda ba aikin mambobin CJTF ba ne.

"Aikinsu shi ne tallafawa jami'an tsaro wajen gudanar da ayyukansu ba wai su yi gaban kansu ba; jami'an tsaro ne kadai ke da ikon yin fito na fito da yan ta'adda," a cewar sa.

Ya bukaci masu rike da sarautun gargajiya a jihar da su gargadi mambobin CJTF akan ayyukan da suka wajaba akansu tare da hana su shiga huruin da ba nasu ba.

Da ya ke jawabi, Sarkin Kauran Namoda, Alhaji Muhammad Asha, ya godewa gwamnatin jihar bisa wannan kokari na ta tare da kuma bada tabbacin yunkurin gwamnatinsa na goyon bayan gwamnatin jihar wajen magance matsalar da ke ciwa jihar tuwo a kwarya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel