Yanzu Yanzu: Buhari zai tafi kasar Jordan a yau

Yanzu Yanzu: Buhari zai tafi kasar Jordan a yau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa Amman a ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu domin amsa gayyatar Sarki Abdullah II bin Al-Hussein na kasar Jordan don halartan taron kungiyar tattalin arziki na duniya wanda za a gudanar a Dead Sea, Jordan.

Shugaba Buhari zai gabatar da wani jawabi yayin bude taron tare da Sarki Abdullahi II bin Al-Hussein da kuma babban sakataren majalisar dinkin duniya, António Guterres.

Daga nan za su hadu da sauran shugabannin tattalin arziki na duniya a wani taron da za a gudanar a cibiyar taro na Sarki Hussein Bin Talal.

Yanzu Yanzu: Buhari zai tafi kasar Jordan a yau

Yanzu Yanzu: Buhari zai tafi kasar Jordan a yau
Source: Twitter

Shugaban kasar zai kuma yi ganawa mai muhimmanci da wasu shugabannin dunniya bayan taron.

Daga nan Buhari zai bar Amman a ranar Lahadi zuwa kasar Dubai domin halartan taron zuba jari na tara da ake yi duk shekara, a ranar 8 zuwa 10 ga watan Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Lalong zai sake gina babban kasuwar Jos na biliyoyin kudi da ya kone

Buhari wanda ya samu gayyata daga mai martaba, Sheikh Mohammed Bin Rachid Al Maktoum, mataimakin Shugaban kasar Dubai, Firai Minista da sarkin dubai, zai zamo bako na musamman a taron, sanann zai yi jawabi mai taken “Mapping the Future of Foreign Direct Investment: Enriching World Economies through Digital Globalization.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel