FG zata samar da aiki ga matasa 60,000 a karkashin wani sabon tsari

FG zata samar da aiki ga matasa 60,000 a karkashin wani sabon tsari

Kwamitin zartar wa na gwamnatin tarayya (FEC) ya amince da fara wani wani sabon tsari da zai samar da aikin yi ga matasan Najeriya da ke tsakanin shekara 18 zuwa 25.

Ministan kasafi da tsare-tsare, Udoma Udo Udoma, ne ya sanar da hakan a yau, Laraba, jim kadan bayan kammala taron FEC da shugaba Buhari ya jagoranta.

Minista Udoma ya ce sunan sabon shirin 'N-Power knowledge multi-track youth empowerment programme'.

Ya bayyana cewar za a bawa matasa 12,000, da suka kammala karatu amma basa aiki, horo a kan sarrafa wa da gyran na'urori masu kwakwalwa da kayan da ke amfani da wutar lantarki daban-daban.

FG zata samar da aiki ga matasa 60,000 a karkashin wani sabon tsari
Udoma Udo Udoma
Asali: Depositphotos

Udoma ya ce shirin, wanda a karkashinsa za a bawa dukkan matasan da suka kammala karatu dama, zai kasance a karkashin tsarin bayar da tallafi ga 'yan kasa domin dogaro da kai (NSIP).

Ya kara da cewa matasa 12,000 da za a bawa horo, za a dora masu alhakin bawa wasu matasan horo da yawansu zai kai 60,000.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tayi magana a kan kisan 'yar Najeriya a kasar Saudiyya

Ya ce an damka kwangilar nev a hannun wani kamfani mai suna Softcome Ltd, wanda zai yi aiki tare da sashen NSIP na gwamnatin tarayya.

Ministan ya bayyana cewar gwamnatin zata kashe N259,000 a kan kowanne matashi yayin da zata kashe masa N207,000 a kan kayan aiki.

Shirin da za a kammala a cikin wata 9, zai lashe zunzurutun kudi da yawansu ya kai N5,595,669,250, kamar yadda ministan ya bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel