Rugum babban motsi: Motar tirela tayi gaba da gaba da jirgin kasa a jahar Jigawa

Rugum babban motsi: Motar tirela tayi gaba da gaba da jirgin kasa a jahar Jigawa

Wata babbar motar daukan kaya tayi gaba da gaba da wani jirgin kasa a daidai inda layin dogo ya ratsa kan titi a cikin karamar hukumar Birniwa ta jahar Jigawa, lallai hatsari ba lallai sai mota da mota ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan karo da karo ya faru ne da sanyin safiyar Talata, 2 ga watan Afrilu a garin Birniwa, sai dai rahotanni sun tabbatar da cewar direban motar ya samu rauni, amma ba dayawa ba.

KU KARANTA: Mutuwa riga: Matashi ya nutse a cikin ruwa a jahar Kano

Rugum babban motsi: Motar tirela tayi gaba da gaba da jirgin kasa a jahar Jigawa
Hatsarin
Asali: UGC

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da cewar lamarin ya faru ne a lokacin da jirgin wanda ya taso daga jahar Kano kuma ya nufin garin Nguru na jahar Yobe don dauko shanu da ake safararsu daga Arewa zuwa kudancin kasar nan.

A daidai wannan lokaci ne sai motar tirelan tayi kokarin tsallaka titin yayin da jirgin shima ya iso mahadar layin dogo da titin, a irin haka, jirgi ya kan yi ta kuwwa tun daga nesa kafin ya iso irin wannan waje don gudun afka ma motoci da masu tafiya akan hanya.

Amma abinka da direbobin Najeriya iyayen ganganci, har sai da jirgin yazo gab, a lokacin ne direban yayi kokarin kaucewa, amma tuni jirgin ya cimmasa, inda ya tsikari bayansa a daidai mahadar layin dogo da titin Hadejia zuwa Nguru.

A wani labarin kuma, masu iya magana suka ce tsautsayi baya wuce ranarsa, kuma dama ai mutuwa rigace, bata fita, kuma tana kan kowa, kamar yadda hakan ta tabbata akan wani matashi mai shekaru 20, Dayyabu Kashim a jahar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa mutuwa ta riski wannan matashi ne yayin da yake shiga cikin wannan korama dake unguwar Dorayi, Ramin Kasa cikin karamar hukumar Gwale ta jahar Kano, yana wanka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel