Idan ajali ya yi kira: Wata rijiya ta ci rayukan mutane hudu a garin Kabba

Idan ajali ya yi kira: Wata rijiya ta ci rayukan mutane hudu a garin Kabba

- Wasu mutane hudu sun gamu da ajalinsu a garin Kabba da ke jihar Kogi bayan bangon wata rijiya ya rufto a kansu

- Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kogi, DSP William Aya, ya tabbatar da faruwan hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN)

- Tsautsayi ya fada kan mutanen ne yayin da matar da rijiyar ke gidanta ta kira su domin su yi mata aikin gyaran rijiyar

Wasu mutane hudu sun rasa ransu a garin Kabba da ke jihar Kogi bayan bangon wata rijiya ya rufto a kansu.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kogi, DSP William Aya, ne ya sanar da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) hakan, ya ce mutane hudun leburori ne, kuma sun gamu da ajalinsu ne yayin gyaran rijiyar.

Tsautsayi ya fada kan mutanen ne yayin da matar da rijiyar ke gidanta ta kira su domin su yi mata aikin gyaran rijiyar.

Da yake magana da NAN ta wayar tarho, Aya ya bayyana sunayen mutanen da suka mutu kamar haka; Kayode Ayeni, Niyi Jimoh, Olusanmi Sunday da Ayo Sunday.

Idan ajali ya yi kira: Wata rijiya ta ci rayukan mutane hudu a garin Kabba
Rijiya
Asali: Twitter

A cewar sa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na ranar Litinin a unguwar Sango da ke garin Kabba.

Kakakin ya ce DPO na ofishin 'yan sanda da ke garin Kabba ya gaggauta aika jami'an 'yan sanda zuwa wurin da abin ya faru bayan samun rahoton afkuwar lamarin.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tayi magana a kan kisan 'yar Najeriya a kasar Saudiyya

Sannan ya kara da cewa, sai da jami'an 'yan sanda suka yi haka a cikin rijiyar kafin su kai ga tono mutanen tare da garzaya wa da su babban asibitin garin Kabba, inda likitoci suka bayar da tabbacin mutuwar su.

Aya ya ce sun ajiye gawar mutanen, da shekarunsu na haihuwa ke tsakanin 30 zuwa 35, a dakin ajiyar gawa na asibitin Kabba.

A cewar Aya, ita kanta matar da ta saka mutanen aikin a sume aka same ta bayan ta fahimci cewar rijiyarta mai zurfin kafa 25 ta rufta a kan mutanen yayin da suke ciki domin gyaran ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel