Shugabancin majalisa: APC bata yi wa kudu maso gabas adalci ba – Kungiyar matasan Igbo

Shugabancin majalisa: APC bata yi wa kudu maso gabas adalci ba – Kungiyar matasan Igbo

Shugabannin wata gamayyar kungiyar matasa na kudu maso gabas, sun bayyana cewa jam’iyyar All Progressive Congress(APC) baya yi wa yan Igbo adali ba, sakamakon kin amincewa da batun mika mukamin shugabanccin majalisar dattawa ga yankin.

Kungiyar sun yi korafin cewa APC na ci gaba da hana wa yankin kudu maso gabas babban matsayi duk da cewar yankin ta bata gagarumin goyon baya ta hanyar zabar sanatoci day an majalisar wakilai fiye da yadda suka yi a 2015.

Sun bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole da su tabbatar da cewa jam’iyyar bata hana kowani yanki hakkinsa ba wajen rabe-raben mukaman kasar.

Shugabancin majalisa: APC bata yi wa kudu maso gabas adalci ba – Kungiyar matasan Igbo
Shugabancin majalisa: APC bata yi wa kudu maso gabas adalci ba – Kungiyar matasan Igbo
Asali: Facebook

A wani jawabi dauke da sa hannun Shugaban kungiyar, Cif Goodluck Egwu Ibem; sakatarenta, Dr. Igwe Kanice da kuma sakataren labaranta, Hon. Joshua Nnamani, kungiyar ta sha alwashin cewa yan Igbo ba za su kuma bari a mayar dasu koma baya ba a tushen su.

KU KARANTA KUMA: Rivers: APC tayi ikirarin cewa babu rashin jituwa tsakanin Ameachi da Oshiomhole

a matsayi na Shugaban majalisar dattawa, Dr. Kalu ya kasance gawurtaccen dan siyasa da ke da karfin da zai iya daukaka bangaren dokoki zuwa tafarkin i gaba. Zai kara daraja da daukaka ga gwamnatin Buhari.

Kungiyar ta bukai APC da ta magance lamarin rashin aldalci da ake yiwa yankin kudu maso gabas domin wanzar da aminci da dorewar Najeriya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel