Farashin Man Fetur ya yi daraja a kasuwar duniya

Farashin Man Fetur ya yi daraja a kasuwar duniya

Mun samu rahoton cewa, karo na farko a shekarar 2019, farashin man fetur ya yi darajar gaske a ranar Talata inda ya yi tashin doron zabuwa a kasuwar duniya da a halin yanzu farashin sa ya kai Dalar Amurka 69 ga kowace ganga.

Darajar man fetur a kasuwar duniya ya bayu a sanadiyar takunkumi na hukunci da kasar Amurka ra shimfida akan kasar Iran da kuma Venezuela da ya haifar da karanci da rashin samuwar man fetur a kasuwannin man fetur na duniya.

Farashin Man Fetur ya yi daraja a kasuwar duniya
Farashin Man Fetur ya yi daraja a kasuwar duniya
Asali: Facebook

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kasar Amurka ta fara shirin tsaurara matakin da ta dauka akan kasar Iran inda a halin yanzu ya rage adadin man fetur da kasar ke fitar wa da kaso 50 cikin 100.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Amurka ta tsaurara matakai akan kasar Venezuela da ta kasance daya daga cikin jerin kasashen duniya da ke sahu na gaba ta fuskar arziki na samar da man fetur.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, cikin sakamakon binciken da aka wallafa a wannan mako, matakin da kasar Amurka ta dauka ya yi daidai da kudiri da kuma manufofi na kasashen duniya masu arziki na samar man fetur.

KARANTA KUMA: Zaben Zamfara: Ba mu da ta cewa sai dai mu bi umurnin Kotu - INEC

Da misalin karfe takwas na safiyar Talata, man fetur ya yi daraja karo na farko a bana yayin da farashin sa ya kai $69.11 kan kowace ganga guda tun bayan da darajar sa ta kai $69.50 a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel