Arewa maso tsakiya ta sa kafar wando daya da APC yayinda Bago ya kaddamar da kudirin takarar kakakin majalisa

Arewa maso tsakiya ta sa kafar wando daya da APC yayinda Bago ya kaddamar da kudirin takarar kakakin majalisa

Yayinda ake tseren neman kujerar kakakin majalisar wakilai, dan majalisar wakilai daga jihar Niger, Mohammed Umaru Bago a ranar Lahadi, 31 ga watan Maris ya kaddamar da kudirinsa na neman kujerar kakakin majalisa.

Da farko dai Shugaban APC ta bayar da matsayin ga yankin kudu maso yamma sannan ta tsayar da Shugaban masu rinjaye a majalisar Femi Gbajabiamila a matsayin zabin jam’iyyar.

Hon Bago ya kaddamar da cewa zai fito a wannan karon ne don gyara rashin adalcin da ake yiwa arewa naso tsakiya wajen rabon mulki a kasar, yayi ikirarin cewa yanki bata taba samar da kakakin majalisa ko mataimakin kakakin majalisa ba tun da aka kafa damokradiyya a kasar tsawon shekaru 20 da suka gabata.

Arewa maso tsakiya ta sa kafar wando daya da APC yayinda Bago ya kaddamar da kudirin takarar kakakin majalisa
Arewa maso tsakiya ta sa kafar wando daya da APC yayinda Bago ya kaddamar da kudirin takarar kakakin majalisa
Asali: UGC

Bago wanda ke a sansanin siyasar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sa jam'iyyar tace lallai sai ta bangaren yanki za a bi wajen zabar shugabanci wanda aka shafe tsawon shekaru 20 ana yi, cewa "Wani gudun mawa yankin kudu maso yamma ta bayar wajen nasarar jam'iyyar a zaben da aka gudanar kwanan nan idan aka kwatanta ta da arewa maso tsakiya? yankin arewa masu tsakiya ta fi ta da kuri'u sama da 500,000, za a iya dubawa dn tabbatar da hakan."

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisar dattawa: Mutanen Borno na tare da Ndume – Jigon APC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kafa wani kwamiti domin bincikar faduwarta a jihar Anambra a lokacin zaben Shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar, 23 ga watan Fabarairu.

A cewar jam’iyyar, adadin kuri’un da jam’ iyyar ta samu a jihar bai yi daidai da tsayuwar siyasar jam’iyyar a jihar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel