Zargin magudi: Za mu karbi kujerar mu a Kotu - APC ta fada wa Tambuwal
Shugaban jam'iyyar APC a jihar Sokoto, Alhaji Isa Sadiq Achida, ya bawa magoya bayan jam'iyyar tabbacin cewar nan bada dadewa ba za mayar wa da APC kujerar gwamnan jihar da jam'iyyar PDP karkashin gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, tayi masu fashin ta.
Hakan na kunshe ne cikin wani jawabi da Achida ya raba ga manema labarai a garin Sokoto ranar Asabar, a matsayin martani ga zargin da jam'iyyar PDP tayi a kan cewar yunkurin APC na yin amfani da karfin gwamnatin tarayya domin murde zaben gwamnan jihar bai yiwu ba.
Acida ya ce, "kage ne da zance irin na siyasa da gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya saba yi, kalaman sa ba za su yi tasiri ba a kan jama'ar jihar Sokoto ba.
"Babu wanda ya dogara ko ya yi amfani da karfin gwamnatin tarayya, dumbin magoya bayan da mu ke da su a kowanne mataki ne su ka yi dafifi wajen fito wa su zabi jam'iyyar APC da 'yan takarar ta a mataki dabn-daban.
"Yadda jama'a su ka fito su ka zabi 'yan takarar APC tun daga kan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nuna cewar su na tare da jam'iyyar.
DUBA WANNAN: Bayan zabe: INEC ta kammala shirin soke wasu jam'iyyu
"Masu zabe basu yarda da jam'iyyar PDP ba saboda ba ta da 'yan takara masu nagarta da ke da goyon bayan jama'a."
Ya bawa masoya da magoya bayan APC tabbacin cewar kotu za ta karbo wa jam'iyyar hakkin ta a karar da za a fara sauraro a kotun sauraron korafin zabe nan bada dadewa ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng