Daruruwan mutane na tururuwa wurin neman maganin bindiga a jihar Zamfara

Daruruwan mutane na tururuwa wurin neman maganin bindiga a jihar Zamfara

Da akwai alamu da su ke nu na cewa, mutanen jihar Zamfara sun fara sarewa da gwamnati akan irin kisan gillar da ake yi musu, hakan ne ma ya sanya da yawa daga cikin su, su ke bazama neman maganin kariya daga bindiga

A kowacce rana daruruwan mutane suna tururuwa zuwa kauyen Tsauni, da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, domin sayan wata laya, wacce su ka yi imanin, in dai su ka yi amfani da ita, to sun fi karfin kowacce irin bindiga.

Mutane da dama daga kowanne sashe na jihar suna zuwa kauyen domin sayen layar, inda suka bayyana cewa amfani da layar ita ce hanya daya tilo da ta rage musu.

Daruruwan mutane na tururuwa wurin neman maganin bindiga a jihar Zamfara
Daruruwan mutane na tururuwa wurin neman maganin bindiga a jihar Zamfara
Asali: Original

Wani mazaunin yankin mai suna Bala Hassan, ya yi bayanin cewa: "Idan mutum ya je wurin, za a ba shi laya guda daya, da ruwa a kofi, zai shanye layar, sannan zai biya naira dari biyu. Bayan kasha za'a gwada harbinka, domin a tabbatar da aikin maganin. Ba a yarda kowa ya tafi da layar gida ba, saboda a ta ke a wurin ake sa ka mutum ya shanye layar."

Majiyarmu LEGIT.NG ta samu rahoton cewa ana makale layar a jikin bishiyane, inda za a bukaci wasu su harbi bishiyar, amma duk harbin da za a yi ba zai sami bishiyar nan ba.

KU KARANTA: An kashe wata mata da diyarta a jihar Kebbi

Haka shi ma wani mai suna Dan Mallam Sani ya ce: "Mutane da dama sun yarda da wannan layar, har ya kai matakin da idan mutane sun gane cewa kasha wannan layar za su fara harbinka, kuma harsashin ba zai taba ka ba. Kuma mun fahimci cewa 'yan ta'addar da suke kawo mana hari, bayan bindigogin da su ke da su, kuma suna amfani da maganin bindiga, domin kare kansu, saboda haka ba za mu ta ba kyalesu su dinga kashe mu ba, babu gyara babu dalili."

Sai dai kuma wani ma'aikaci a jami'ar Katsina, Sani Sa'adu, ya bayyana cewa ya kamata gwamnati ta wayarwa da masu zuwa shan maganin bindiga kai, saboda hakan ba shine mafita ba akan wannan lamari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel