Shugaba Buhari zai rage albashin wasu ma'aikata a kasar nan

Shugaba Buhari zai rage albashin wasu ma'aikata a kasar nan

- A dai-dai lokacin da ake shirin karawa ma'aikata albashi, sai gashi kuma za a ragewa wasu ma'aikatan nasu albashin

- Shugaban kasar kuma ya jadda kudurin shi na mayar da albashin ma'aikata N30,000 mafi karanci

Kamar yanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shirya tsaf domin gabatar da sabon tsarin albashi a kasar nan, alamu masu karfi suna nuna cewar hakan zai shafi wasu ma'aikata a kasar nan, inda za'a iya rage musu albashin su.

Ma'aikatun da abin zai shafa sun hada Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Babban Bankin Najeriya (CBN) da kuma ma'aikatar amsan kudin shigar tarayya (FIRS).

Hakan ya biyo bayan rahoton da shugaban kasar ya karba daga hannun kwamitin da aka nada akan karin albashin ranar Litinin dinnan data gabata.

Gwamnatin tarayya na shirin rage albashin ma'aikatan NNPC, CBN da FIRS
Gwamnatin tarayya na shirin rage albashin ma'aikatan NNPC, CBN da FIRS
Asali: UGC

A cikin tsarin da shugaban kasar ya baiwa kwamitin karin albashin, sun hada da, da zarar an gama da matsalar karin albashi, gwamnati zata fara neman hanyar da zata bi domin ragewa ma'aikatan da suke daukan albashi fiye da yanda doka ta tsara.

KU KARANTA: Najeriya na bukatar N10trn don habaka tattalin arziki - Fashola

Shugaban kasar yace yana da kyau a sanar da ma'aikatan, saboda kada lokaci yazo da za'a rage musu albashi suga kaman ba'a kyauta musu ba.

"Na san kunyi iya bakin kokarinku wurin ganin an gabatar da dokar karin albashin nan," inji shugaba Buhari, a lokacinda yake magana da 'yan kwamitin, wanda suka hada shugaban ma'aikatar amsan kudin shigar tarayya FIRS, Dr. Babatunde Fowler, da kuma tsohuwar shugabar ma'aikatar amsan kudin shigar tarayya FIRS, Mrs. Ifueko Omoigui-Okauru, Farfesa Akpan Ekpo da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel