Wamakko da Ahmed Aliyu sun musanta kiran Gwamna Tambuwal a waya

Wamakko da Ahmed Aliyu sun musanta kiran Gwamna Tambuwal a waya

- Sanata Aliyu Wammako da kuma dan takaran gwamna a jam’iyyar, Ahmed Aliyu, sun musanta jita-jitan da da ake yadawa cewa sun kira Gwamna Aminu Tambuwal bayan ya lashe zabe

- Hukumar zabe mai zaman kanta dai ta bayyana Tambuwal a matsayin wanda ya sake lashe zaben jihar Sokoto a karo na biyu

Jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wammako da kuma dan takaran gwamna a jam’iyyar, Ahmed Aliyu, sun musanta jita-jitan da ake yadawa cewa sun kira Gwamna Aminu Tambuwal kan zabe da aka sake a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

Jawabin na kunshe na a wani jawabi dauke da sa hannun shugaban kungiyanr yakin neman zaben dan takaran APC, Alhaji Muhammadu Dingyadi, sannan ya bayyana wa yan jarida a Sokoto.

Wamakko da Ahmed Aliyu sun musanta kiran Gwamna Tambuwal a waya
Wamakko da Ahmed Aliyu sun musanta kiran Gwamna Tambuwal a waya
Asali: Twitter

Jawabin ya zo kamar haka: “Sanata Wamakko da dan takaranmu, Alhaji Aliyu basu kira Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ba, kuma basu taya shi murna ba akan nasaran da yayi kamar yanda ake yadawa a kafofin watsa labarai.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta soke zaben fidda gwani na APC a Zamfara

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, dan takaran gwamna jihar Sokoto karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC, Ahmed Aliyu, da Sanata Aliyu Wamakko, sun kira gwamna Aminu Tambuwal na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP domin tayasa murnar nasarar zabe.

Shafin Tuwitan gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana hakan ne bayan hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zama kanta watau INEC ta alanta gwamna Aminu Tambuwal matsayin wanda ya lashe zaben. Ya kada Ahmed Aliyu da tazarar kuri'u 342.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel