Sake zaben Gwamna: Hukumar INEC na karfafa ta’addanci - Tsohon kwamishinan Kano

Sake zaben Gwamna: Hukumar INEC na karfafa ta’addanci - Tsohon kwamishinan Kano

- Kwamishinan fili na jihar Kano a lokacin gwamnatin Kwankwaso, Alhaji Yusuf Bello Danbatta ya zargi hukumar zabe da karfafa ta'addanci da sunan damokradiyya

- Danbatta ya bayyana hakan yayinda yake bayyana ra’ayinsa akan sakamakon zaben da aka sake a jihar Kano

- Sai dai kwamishinan zabe na jihar, Riskuwa Arabu Shehu, ya karyata zargin, inda yake cewa ba a kafa hukumar INEC don tashin hankali ba

Rahotanni sun kawo cewa an bayyana hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), a matsayin cibiya dake karfafa ta’addanci da sunan damokardiyya.

Wani tsohon kwamishinan fili a karkashin gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Alhaji Yusuf Bello Danbatta, ya bayyana hakan a wani jawabin da yayi a ranar Lahadi, 14 ga watan Maris yayinda yake bayyana ra’ayinsa akan sakamakon zaben da aka sake a jihar Kano.

Sake zaben Gwamna: Hukumar INEC na karfafa ta’addanci - Tsohon kwamishinan Kano
Sake zaben Gwamna: Hukumar INEC na karfafa ta’addanci - Tsohon kwamishinan Kano
Asali: UGC

Dambatta, wanda ya bayyan ra’ayinsa a cibiyar hada sakamakon zabe, yayi zargin cewa ba a gudanar da zabe ba a Gama da wassu wuraren da aka shirya gudanar da zaben.

Yayinda yake mayar da martani akan zargin, kwamishinan zabe na jihar, Riskuwa Arabu Shehu, ya karyata zargin, inda yake cewa ba a kafa hukumar INEC don tashin hankali ba.

Shehu ya ce a tsare-tsaren hukumar ta tanadi ka’idoji akan yanda ya kamata hukumar ta magance tashe-tashen hankula.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta soke karar da ke neman a dakatar da hada sakamakon Bauchi

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wata kungiya mai zaman kan-ta mai suna Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC), ta nuna rashin jin dadin ta game da yadda aka gudanar da zaben cike-gibi a jihar Kano cike da rikicin 'Yan daba.

Wannan kungiya tayi tir da yadda jami’an tsaro su ka gaza maganin rikicin daba da ya rincabe a lokacin zaben. Kungiyar tace masu kada kuri’a sun gamu da barazana iri-iri a wajen zaben da aka yi na cike gibi a Ranar Asabar 23 ga Watan Maris.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel