2019: Sufetan ‘Yan Sanda ya aika DIG Anthony Michael domin lura da zaben Kano

2019: Sufetan ‘Yan Sanda ya aika DIG Anthony Michael domin lura da zaben Kano

Bisa dukkan alamu an samu baraka a game da sha’anin tsaro a zaben cike-gurbi da ake yi a jihar Kano. Wannan yayi sanadiyyar da manyan ‘yan daba su ka cika inda ake gudanar da zaben na gwamna.

Jaridar Daily Nigerian tace an samu matsalar ne a dalilin maida Kwamshinan ‘Yan Sanda na jihar watau Mohammed Wakili saniyar ware da aka yi. Hakan ya faru ne a dalilin turo wani babban jami’in ‘yan sanda zuwa jihar Kano jiya.

A daf da karshen makon nan ne Sufeta Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu ya aika wasu manyan mataimakin Sufeta na DIG har 5 domin su lura da zabukan cike-gurbi na Gwamnoni da za ayi a wasu jihohi 5 a Ranar Asabar din yau.

Kamar yadda mu ka samu labari, a Ranar Juma’a da dare 23 ga Watan Maris dinnan ne DIG Anthony Michael ya isa Kano. Sai dai alamu sun nuna cewa Anthony Michael ya wargaza duk shirye-shiryen da CP Mohammed Wakili yayi a da.

KU KARANTA: Wasu manyan ‘Yan daba sun hana jama’a yin zabe a Jihar Kano

2019: Sufetan ‘Yan Sanda ya aika DIG Anthony Michael domin lura da zaben Kano
Anthony Michael ya rusa lissafin Kwamishina 'Yan Sanda a zaben Kano
Asali: Depositphotos

Jaridar tace an yi amfani da sabon shugaban jami’an ‘yan sandan wajen shigowa da ‘yan daba cikin Garin Kano. A irin su Yelwa da ke cikin karamar hukumar Dala, an samu gungun ‘yan daba da aka yi kokarin shigo da su cikin Unguwar.

Haka zalika a irin su Nasarawa, Madobi, Gwarzo da kuma Doguwa da sauran wuraren da aka shirya gudanar da zabe, ‘yan daba sun rika cin karen su babu babbaka ba tare da ‘yan sanda sun yi wani abu ba kamar yadda su ka yi a baya ba.

Jami’an tsaron na ‘yan sanda ta bakin Haruna Kiyawa, sun tabbatar da cewa an samu bazuwar ‘yan daba da makamai a cikin Garin Kano, amma sun sha alwashin cewa za su yi kokarin ganin an zauna lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel