Zaben Kano: INEC ta shirya ma zabe a kananan hukumomi 28

Zaben Kano: INEC ta shirya ma zabe a kananan hukumomi 28

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a jihar Kano tace ta kammala shiri tsaf domin gudanar da zaben gwamna da za a sake a fadin kananan hukumomi 28 da ke jihar.

Kwamishinan zabe na jihar, Farfesa Riskuwa Arab-Shehu ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, 21 ga watan Maris a Kano gabannin zaben da za a sake yi a ranar Asabar, 23 ga watan Maris.

A cewarsa, a fadin kananan hukumomin 28, akwai ciniyoyin rijista 75, mazabu 207 da kuma wuraren zabe 276 da yawan adadin masu rijista 128,324.

Arab-Shehu yayi bayanin cewa an soke zabe a fadin kananan hukumomi 15 ne saboda rikici sannan mazabu 116 abun ya shafa, ya kara da cewa yankunan da abun ya shafa na da masu zaben 73,173.

Zaben Kano: INEC ta shirya ma zabe a kananan hukumomi 28
Zaben Kano: INEC ta shirya ma zabe a kananan hukumomi 28
Asali: UGC

Ya ci gaba da cewa, “A kananan hukumomi 23, an soke zabe saboda zarcewar zabe da kuma rikici day a barke a gudanarwar zabe a wadannan yankuna.

“A wadannan yankuna sa abun ya shafa, muna da masu zabe 55,151 da aka yi wa rijitsa a mazabu 92 da ke fadin kananan hukumar da abun ya shada.

“Da fari, muna da kananan hukumomi 29 da abun ya shafa, amma daga baya sai muka lura cea, Bunkure inda ba a yi amfani da na’urar tantance kuri’u ba na daya daga cikin mazabun, don haka aja kaddamar da shi a matsayin marasa amfani maimakon sokewa,” inji shi.

Arab-Shehu ya karaa da cewa hukumar bayan gudanar da zabe a ranar 23 ga watan Fabrairu, ta sake duba dukkanin mazabunda abun ya shafa sannan ta gano ainahin adadin kananan hukumomin da abun ya shafa.

A cewarsa, hukumar zabe ta karbi dukkanin kayayyakin sake zaben inda ya bayyana cewa za a fara rabon kayayyakin a ranaar Juma’a.

KU KARANTA KUMA: Sake zabe: IGP ya tura manyan jami’ai 23 domin sanya idanu a mazabu a fadin kasar

Ya ba dukkanin jam’iyyun siyasa tabbacin cewa INEC za ta yi iya bakin kokarinta don tabbatar da adalci da gaskiya a zaben da za a sake a jihar.

Arab-Shehu ya baayyana cewa an turo kwamishinonin zabe daga Ogun, Kebbi da Zamfara zuwa Kano domin su tallafa masa a gudanarwar zaben da za a sake a ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel